Yan Bindiga Sun Kai Wani Sabon Hari Jihar Benuwai, Sun Hallaka Mutane da Dama

Yan Bindiga Sun Kai Wani Sabon Hari Jihar Benuwai, Sun Hallaka Mutane da Dama

- Wasu yan bindiga sun kashe mutum 11 a ƙauyukan jihar Benuwai yayin da suka bar wasu da raunuka

- Rahotanni sun nuna cewa ƙauyuka biyu ne harin ya shafa kuma dukkan su a yankin ƙananan hukumomi daban-daban

- Kakakin hukumar yan sandan jihar Benuwai, DSP Catherine Anene, tace har yanzun bata samu bayani kan lamarin ba

Yan bindiga sun kashe mutum 11 a wani sabon hari na daban da suka kai ƙauyukan jihar Benuwai, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Yan bindigan sun kai harin ne ƙauyen Anyom dake gundumar Mbatyula, ƙamar hukumar Katsina Ala, da kuma ƙauyen Zango-Akiki na gundumar Mbalagh, ƙamar hukumar Makurɗi.

KARANTA ANAN: An Kashe Mutum 500 Tare da Sace Wasu 201 a Mazaɓar da Nake Wakilta, Ɗan Majalisa

Wani shaida ya bayyana cewa an gano gawarwakin mutane 5 a ƙauyen Zango-Akiki kuma an riga an kai su asibitin Makurɗi, yayin da har yanzun ake neman wasu mutum 5.

Yan Bindiga Sun Kai Wani Sabon Hari Jihar Benuwai, Sun Hallaka Mutane da Dama
Yan Bindiga Sun Kai Wani Sabon Hari Jihar Benuwai, Sun Hallaka Mutane da Dama Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Shaidan ya ƙara da cewa maharan sun kai farmaki ƙauyen Zango-Akiki wanda ke bayan barikin sojoji da safiyar ranar Alhamis, inda suka hallaka mutum 5 kuma suka jikkata wasu da dama.

Hakanan kuma, sakataren hulɗa da jama'a na ƙaramar hukumar Katsina Ala, Tertsea Benga, ya tabbatar da cewa an kashe mutum 6 a ƙauyen Anyom, jumulla mutum 11 kenan a dukkan hare-haren.

Benga yace: "Yan bindigan sun kai hari gonakin mutanen ƙauyen, inda suka bar shanun su suna cinye amfanin gonakin mutanen ƙauyen, suka kashe wasu sannan suka yi awon gaba da mata. Har yanzun ba'a san inda wasu suke ba."

KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Fallasa Shirin da Aka Yi Domin Hamɓarar da Gwamnatinsa

Ya ƙara da cewa maharan sun kai hari ƙauyen ne da misalin ƙarfe 3-4 na yammacin Laraba, an tabbatar da mutuwar mutum 6 a harin yayin da ake cigaba da neman waɗanda suka ɓata.

Da aka nemi kakakin hukumar yandan jihar, DSP Catherine Anene, tace har yanzun bata samu rahoto a kan faruwar lamarin ba.

A wani labarin kuma Yaƙi da Cin Hanci a Mulkin Demokaraɗiyya Yana da Matuƙar Wahala, Buhari

Shugaba Buhari ya koka da wahalar yaƙi da cin hanci da rashawa a mulkin demokaraɗiyya, kamar yadda daily nigerian ta ruwaito.

Shugaban yace tun sanda aka zaɓe shi a matsayin shugaba shekara 6 da ta wuce yake shan wahala wajen yaƙar masu cin hanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel