An Kashe Mutum 500 Tare da Sace Wasu 201 a Mazaɓar da Nake Wakilta, Ɗan Majalisa
- Wani ɗan majalisar wakilai ya koka ga takwarorinsa kan matsalolin tsaron da yan mazaɓarsa ke ciki yayin zaman su na Laraba
- Ɗan majalisa daga jihar Kebbi, Kabir Ibrahim Tukura, yace an kashe sama da mutum 500 tare da sace wasu 201
- Yace yan bindiga sun saka mutanen yankin cikin wani mummunan hali, inda suke ƙona musu gidaje
Ɗan majalisar wakilai na tarayya daga jihar Kebbi, Kabir Ibrahim Tukura, ya faɗawa zauren majalisa ranar Laraba cewa an kashe sama da mutum 500, an sace mutum 201.
Sannan kuma an tilasta wa 15,000 barin muhallinsu a hare-haren yan bindiga da ayyukan ta'addanci a ƙauyukan da ake noma a ƙaramar hukumar Sakaba da Danko/Wasagu, jihar Kebbi.
KARANTA ANAN: FG Ta Kafa Sabbin Sharuɗda 3 Kan Twitter, Facebook da Instagram Ko Ta Hana Amfani da Su
Sai dai bai fayyace lokacin da aka kai hare-haren ba, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
A wata mahawara da ya jagoranta yayin zaman majalisar, Tukura yace ta hanyar jami'an yan sanda ya tabbatar da an kashe mutum 88 a harin da aka kai makon da ya gabata.
A cewarsa harin ya shafi ƙauyukan Koro, Kimi, Gaya, Dimi, Zulu, Rafin Gora, Dan lanko, Dguenge, Chonoko, da Unashi, ƙaramar hukumar Danko/Wasagu.
Ya kuma ƙara da cewa an sake gano gawar wasu 150 a sabon binciken da aka gudanar a yankunan da aka kai harin.
Tukura yace rahoto ya nuna cewa an yi awon gaba da shanu kimanin 5,000 da awaki 3,000 a waɗannan yankunan da aka kai hari makon da ya gabata.
KARANTA ANAN: Yan Majalisar Wakilai Sun Buƙaci Shugaban Hukumar FIRS Yayi Murabus Daga Muƙaminsa
A wani sashin maganganun Tukura, yace:
"A wasu lokuta, yan bindiga suna ƙona gidajen mutane, hakan yana tilasta musu neman matsuguni, sannan kuma da yawan matan su da yayan su an ci mutuncin su."
"Duba da yanayin matsalar tsaro a Danko/Wasagu da Sakaba da kuma ƙasa baki ɗaya. Waɗan nan yankuna suna cikin tashin hankali da yan bindiga suka jefa su a ciki."
"An ƙashe sama da mutum 500 tare da sace mutum 201, inda aka biya miliyoyi a matsayin kuɗin fansa duk a waɗannan ƙananan hukumomin."
A wani labarin kuma Gwamnatin El-Rufa'i Tayi Magana Kan Cafke Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban Greeenfield
Gwamnatin jihar Kaduna ta yi bayani game da rahoton dake yawo cewa an kama yan bindigan da suka sace ɗaliban Greenfield.
Kwamishinan tsaro na jihar, Samueƙ Aruwan, yace gwamnati bata labarin kama yan ta'addan.
Asali: Legit.ng