FG Ta Kafa Sabbin Sharuɗda 3 Kan Twitter, Facebook da Instagram Ko Ta Hana Amfani da Su

FG Ta Kafa Sabbin Sharuɗda 3 Kan Twitter, Facebook da Instagram Ko Ta Hana Amfani da Su

- Gwamnatin Najeriya ta kafa wasu sharuɗɗa uku akan duk wata kafar sadarwa dake Najeriya

- Ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, shine ya bayyana haka ga manema labarai bayan twitter ya nemi sasanci

- Gwamnati tace dole ne kowace kafar watsa labarai ko ta sada zumunta ta mallaki lasisi

Gwamnatin tarayya ta umarci dukkan kafofin watsa labarai da dandalin sada zumunta su mallaki lasisin gudanar da aikin su, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yan Majalisar Wakilai Sun Buƙaci Shugaban Hukumar FIRS Yayi Murabus Daga Muƙaminsa

Ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, yace dandalin sada zumunta kamar Facebook, intagram da twitter ya wajaba a kansu su yi rijista.

Ministan ya bayyana hakane yayin jawabi ga manema labaran gidan gwamnati bayan taron majalisar zartarwar ta tarayya, kamar yadda the cable ta ruwaito.

FG Ta Kafa Sabbin Sharuɗda 3 Kan Twitter, Facebook da Instagram Ko Ta Hana Amfani da Su
FG Ta Kafa Sabbin Sharuɗda 3 Kan Twitter, Facebook da Instagram Ko Ta Hana Amfani da Su Hoto: dailytrust.ng
Asali: UGC

Yace kamfanin twitter sun nemi gwamnatin tarayya domin a tattauna a samu masalaha.

Da aka tambaye shi ko gwamnati zata amince ta zauna teburin sulhu da kamfanin twitter? Lai Muhammed Yace:

"Me zai hana? Mun riga mun faɗi sharuɗɗan mu. Na farko, domim yin kasuwanci a Najeriya, wajibi su yi rijista a matsayin kamfanin Najeriya."

"Na biyu, Wajibi ne gare su, su mallaki lasisin gudanar da ayyukan su a Najeriya."

"Na uku, Wajibi ne dandalin sada zumunta ya hana ayyukan da suke barazana ne ga kasancewar Najeriya ɗaya, idan suka yi wannan , bamu da matsala da su, mun riga mun faɗa musu haka."

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin El-Rufa'i Tayi Magana Kan Cafke Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban Greeenfield

Ministan ya ƙara jaddada cewa babban dalilin dakatar da twitter shine kamfanin ya samar da hanya ga waɗanda suke barazana ne ga zaman lafiyar Najeriya da kuma kasancewarta ƙasa ɗaya.

A wani labarin kuma FG Ta Fito da Wani Sabon Tsari, Zata Tallafawa Yan Najeriya Miliyan Ɗaya da N5,000 na Tsawon Wata 6

Gwamnatin tarayya zata tallafawa yan Najeriya kimanin miliyan ɗaya da kuɗi N5,000 na tsawon watanni 6.

Gwamnatin tace an kaddamar da shirin tun farkon wannan shekarar kuma wasu mutane sun amfana da shi a Lagos da Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel