Buhari ya sha yabo bayan ƙaddamar da layin dogo na Legas zuwa Ibadan da aka kashe fiye da N600bn wurin ginawa

Buhari ya sha yabo bayan ƙaddamar da layin dogo na Legas zuwa Ibadan da aka kashe fiye da N600bn wurin ginawa

- Layin dogo na $1.5 biliyan (N616,005,000,000.00) da ya tashi daga Legas zuwa Ibadan da Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar ya dauki hankalin mutane a intanet

- An wallafa kyawawan hotunan layin dogon da tashar jiragen kasar a dandalin sada zumunta kuma yan Nigeria sun tofa albarkacin bakinsu

- Tashar ta Mobolaji Johnson itace tashar jirgin kasa mafi girma a nahiyar Afirka ta Yamma wacce ke iya daukan fasinjoji 6,000

A yau Alhamis 10 ga watan Yuni ne Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi jihar Legas domin kaddamar da wasu ayyuka ciki har da katafaren layin dogo na Legas zuwa Ibadan mai tsawon kilomita 156.

Kyawawan hotunan layin dogon na zamani da Shugaba Buhari ya kaddamar ya dauki hankulan mutane inda kowa ya rika tofa albarkacin bakinsa.

Kyawawan hotunan layin dogo daga Legas zuwa Ibadan da Buhari ya kaddamar sun burge mutane
Kyawawan hotunan layin dogo daga Legas zuwa Ibadan da Buhari ya kaddamar sun burge mutane. Hoto: Bura-Bari Nwilo
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun cafke hatsabibin matsafin da ke yi wa 'yan IPOB asiri

Layin dogon da tashar jirgin kasa da aka saka wa suna Mobolaji Johnson Station mai daukan mutane 6,000 shine mafi girma a Afirka ta Yamma.

Buhari Sallau, hadimin Shugaban kasa a bangaren watsa labarai ya wallafa hotunan tashar jirgin kasar da layin dogon a shafinsa na Facebook.

Wani dan Nigeria mai suna Bura-Bari Nwilo shima ya wallafa hotunan yana mai yabawa Shugaba Buhari da Minista Rotimi Amaechi saboda kyakyawan aikin da suka yi.

Ya rubuta:

"Wannan kyakyawan aiki ne da zai amfani kowa duk matsayin mutum.
"Yana da kyau a yabawa Minista, Hon Amaechi saboda aikin da ya yi da Shugaban kasa, M. Buhari da ya sakar masa mara don yin aikin. Ina fatan za a maimaita irinsa a wasu sassan kasar."

Wani dan Nigeria mai suna Ayo Ojeniyi shima ya wallafa hotunan aikin.

Kazalika, yan Nigeria sun tofa albarkacin bakinsu.

KU KARANTA: Buhari: Ainihin dalilin da yasa na naɗa Yahaya shugaban sojoji na tsallake na gaba da shi

Kabir Oyewumi Akinola ya ce:

"Mun gode PMB saboda wannan aikin da ka yi amma rashin tsaro na shafar mu matuka."

Gabriel Adewumi Adegoke ya ce:

"Nigeria za ta daukaka, na yi imanin komai zai koma yadda ya ke."

A wani rahoton daban kun ji cewa Yinusa Ahmed, dan majalisar wakilai na kasa daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya ce an fara ganin alherin dakatar da shafin sada zumunta na Twitter da gwamnatin Nigeria ta yi, The Cable ta ruwaito.

Within Nigeria ta ruwaito cewa ya ce abubuwan da yan Nigeria ke yi a dandalin na haifar da rigingimu ne a kasa amma yanzu kura ta fara lafawa sakamakon dakatarwar da gwamnati ta yi.

Ahmed ya yi wannan jawabin ne yayin hira da aka yi da shi a shirin Sunrise Daily a gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel