Ku taimaka ku ceci Najeriya: NCF ta roki Gowon, sauran tsoffin shugabanni

Ku taimaka ku ceci Najeriya: NCF ta roki Gowon, sauran tsoffin shugabanni

- Kungiyar NCFront ta roki tsoffin shugabannin kasa a Najeriya da su taso don ceto kasar daga halaka

- Kungiyar ta bayyana bukatar hannun tsoffin shugabannin saboda kwarewarsu da kuma sanin kasar

- Hakazalika kungiyar ta yi kira ga hadin kai tsakanin 'yan kasa don kaucewa halin da ake fuskanta

Sakamakon rikice-rikicen rashin tsaro a kasar, kungiyar tuntuba ta kasa (NCFront), karkashin jagorancin Alhaji Ghali Umar Na'Abba da Farfesa Pat Utomi, sun roki tsoffin Shugabannin kasa da su “kwato Najeriya daga yakin basasa da ke tafe.”

A wata sanarwa da Karamin Ministan Tsaro (Navy), Dokta Olu Agunloye ya karanta a karshen taron da ta yi jiya a Abuja, kungiyar ta ce:

“Muna kira ga dattijan kasa da su dakatar da hutunsu na dan lokaci tare da daukar nauyin ceton Najeriya daga hallaka gaba daya.

KU KARANTA: APC ta gargadi 'yan Najeriya kan illolin amfani da VPN wajen hawa Twitter

Ku taimaka ku cece Najeriya: NCF ta roki Gowon, sauran tsoffin shugabanni
Ku taimaka ku cece Najeriya: NCF ta roki Gowon, sauran tsoffin shugabanni Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Dangane da wannan, tsoffin Shugabannin kasa, tsoffin shugabannin hafsoshin soja da sauransu za a sanya su a cikin Kwamitin Dattawan Kasa."

Kungiyar ta kira yi Janar Yakubu Gowon da ya yi kiran taron gaggawa na tsoffin shugabbanin kasa da shugabannin jihohi da mataimakansu da sauran jigogi da suka yi ritaya don samar da mafita ga matsalolin da ke dumfaro kasar.

An kuma kalubalanci 'yan kasa da su tashi tsaye don ceton kasar mai yawan jama'a daga shiga halaka ta hanyar sasantawa da duk bangarorin da ke rikici, The Guardian ta ruwaito.

Sassan da dama na Najeriya na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro, yayin da wasu ke fafutukar yadda za su yi su balle daga kasar ta Najeriya baki daya.

Yankin Yarbawa na kokarin ballewa, yayin da yankin Biafra ke kan gaba wajen ganin sun balle daga kasar.

Sai dai, yankunan masu kusanci da juna ba su amince da manufofin junansu, yayin da yankin yarbawa ya gargadi yankin Biafra da tsoma baki a lamurransu.

KU KARANTA: Makinde: A bamu dama mu damka wa 'yan bangan Amotekun bindigar AK-47

A wani labarin, Jami'an tsaro na soji, 'yan sanda da sojin sama sun lalata daya daga cikin sansanonin kungiyar tsaro ta Gabas da ke da alaka da 'yan asalin yankin Biafra, Punch ta ruwaito.

Lalacewar ta afku ne a Amii-Akabo, da ke karamar hukumar Ikeduru ta jihar, biyo bayan kashe shugaban kungiyar ‘yan bindiga a jihar, wanda aka fi sani da Dragon.

Majiyar ‘yan sanda ta shaida cewa daya daga cikin 'yan kungiyar, Osinachi Stanley, ya jagoranci sojoji zuwa sansanin inda aka ceto wata mata ’yar sanda mai mukamin sufeto da ke tsare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel