Majalisa na zargin NIRSAL da yin sama da fadi da N105bn kudin manoma

Majalisa na zargin NIRSAL da yin sama da fadi da N105bn kudin manoma

- Majalisar wakilai za ta gudanar da bincike kan hukumar NIRSAL bisa zargin yin sama da fadi da wasu kudi

- Majalisar na zargin hukumar ne da cinye kudin da gwamnati ta bayar a ba manoma a fadin bashi

- A baya Ministan Shari'a, Abubakar Malami, SAN ya bukaci a gudanar da bincike kan hukumar ta NIRSAL

Majalisar wakilai ta yanke shawarar gudanar da bincike kan zargin karkatar da kudin rancen noma na Naira biliyan 105 da hukumar NIRSAL ta yi.

Chike Okafor, wanda ya fito daga jihar Imo, ya yi wannan zargin ne a ranar Laraba yayin da yake daukar nauyin wani kudiri na binciken jimillar bashin Naira biliyan 275 da aka amince wa manoman kasar nan.

Jaridar TheCable ta tuntubi NIRSAL domin jin ta bakin ta game da zargin.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Kasar Morocco ta halasta noman tabar wiwi a fadin kasar

Majalisa na zargin NIRSAL da yin sama da fadi da N105bn kudin manoma
Majalisa na zargin NIRSAL da yin sama da fadi da N105bn kudin manoma Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Da yake jagorantar mahawarar a yayin zaman na ranar Laraba, Okafor ya ce Najeriya ba ta samu wadatar abinci ba duk da amincewar da aka yi a ba manoman bashi.

Ya ce gwamnatin tarayya ta amince da “bayar da kudade ga manoma a cikin tsare-tsare daban-daban har na sama da Naira biliyan 275”, tun daga tsarin bada rancen noma na kasuwanci (CACS) zuwa shirye-shirye da ke karkashin NIRSAL.

"Baya ga karuwar wadataccen abinci, tsarin shi ne bayar da rancen kudin noma ga manya da kananan manoma 'yan kasuwa don rage farashin kayayyakin amfanin gona, samar da aikin yi da kara samun kudaden shiga," in ji shi.

“Tun bayan amincewar, yawancin manoma ba su samu damar samun rancen ba saboda tsananin da bankuna suka saka ga masu son karbar bashi da kuma zargin almubazzaranci da sama da Naira biliyan dari da hamsin da aka ware wa manoma ta hanyar kamfanin NIRSAL.

"[Kuma] samar da abinci bai kai matsayin da ake tsammani ba duk da amincewar da aka yi wa manoma da sama da biliyan N275.”

A baya cikin shekarar 2020, Ministan Sharia, kuma Babban Lauyan Najeriya ya bukaci hukumomi ciki har da EFCC da su gudanar da bincike kan hukumar ta NIRSAL, This Day ta ruwaito.

AGF din a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Dakta Umar Jibrilu Gwandu, Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Yada Labarai da Hulda da Jama’a, ya ce ya samu takardar koke cewa hukumomi biyar suna gudanar da bincike a kan hukumar.

KU KARANTA: Jinkirta Sallar Asuba ya sa Sheikh Sudais ya tube shugaban limamai a Saudiyya

A wani labarin, Wasu bankuna sun sanar da kwastomominsu cewa za su fara cajin su N6.98 a kowane mu’amala ta USSD da suka yi, Punch ta ruwaito.

Sai dai, masana sun ce yawan cajin da bankuna ke yi na iya zama barazana ga shigar da kudi. A cewarsu, zai kara hada-hadar kudi a hannu saboda yawancin kwastomomin banki za su guji amfani da USSD a ma'amalolin yau da kullum.

Hakazalika, akwai yiyuwar hakan ya sanyaya gwiwar bangaren mutanen da ba su da asusun banki saboda ba za su so biyan irin wadannan kudade a kan 'yan kudaden da za su ajiye ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel