Wata sabuwa: Kasar Morocco ta halasta noman tabar wiwi a fadin kasar

Wata sabuwa: Kasar Morocco ta halasta noman tabar wiwi a fadin kasar

- Bayan duba da wasu dalilai na tattalin arziki, kasar Moroco ta halarta noman wiwi a fadin kasar

- Hakazalika ta bayyana cewa, halastawar zai taimaka wajen dago tattalin arzikin kasar idan aka yi noman a kasuwance

- Kasashen Afrika da dama na kokarin ganin sun halasta noman na wiwi domin inganta tattalin arzikinsu

Majalisar dokokin kasar Morocco ta amince da dokar da ta halatta noman tabar wiwi a kasar don magani da kuma amfanin masana'antu, BBC ta ruwaito.

Manufar matakin ita ce shiga kasuwar duniya da bunkasa noma da samar da ayyukan yi a yankunan karkara.

Morocco tana daya daga cikin manyan kasashe masu samar da tabar wiwi don haramtacciyar hanya, da kuma domin shakatawa. Wannan zai kasance ba bisa doka ba a karkashin sabuwar dokar.

KU KARANTA: Jinkirta Sallar Asuba ya sa Sheikh Sudais ya tube shugaban limamai a Saudiyya

Wata sabuwa: Kasar Mooco ta halasta noman tabar wiwi a fadin kasar
Wata sabuwa: Kasar Mooco ta halasta noman tabar wiwi a fadin kasar Hoto: bbc.com
Asali: UGC

A shekarar da ta gabata, Ruwanda ta ba da izinin samarwa da sarrafa tabar wiwi da nufin kara yawan ribar da take samu.

Gwamnatin Ruwanda ta sake nanata cewa samar da ita da amfani da ita zai takaita ne ga dillalai masu lasisi kamar kantin magani haka kuma shan wiwi zai ci gaba da kasancewa ba bisa ka'ida ba.

A Afirka ta Kudu, har yanzu gwamnati na ci gaba da shirye-shirye don tabbatar da cewa kasar za ta iya karuwa daga shuka ta hanyar mayar da tabar ta zama kasuwanci mai amfani, Africa News ta ruwaito.

A nan gida Najeriya kuwa, Majalisar Wakilai ta shirya zaman halatta amfani da tabar wiwi a kasar don amfanin tattalin arziki, Vanguard ta ruwaito.

KU KARANTA: Da dumi: dumi: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da matan aure 3 a jihar Kaduna

Ba wani labarin, Seyi Makinde, gwamnan jihar Oyo, ya ce idan doka ta yarda, zai gwammace jami'an bangan Amotekun, su dauki bindigogin AK-47 don bunkasa ayyukan tsaro, The Cable ta ruwaito.

Gwamnan ya fadi haka ne a jawabin da ya gabatar a garin Ibadan ranar Talata a wajen bude taron dimokiradiyya na kasa mai taken, "Makomar dimokuradiyya a Najeriya."

Gwamnan ya ce nasarorin da kungiyar ta samu ya zuwa yanzu ya samo asali ne daga tsarin daukar ma'aikata wanda ya tabbatar da cewa an zabi masu gudanar da aikin daga manyan hukumominsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.