Wata Ɗalibar Jami'ar BUK Ta Rigamu Gidan Gaskiya a Gidan Kwanan Ɗalibai

Wata Ɗalibar Jami'ar BUK Ta Rigamu Gidan Gaskiya a Gidan Kwanan Ɗalibai

- Wata ɗaliba dake ajin ƙarshe a jami'ar BUK Kano ta rigamu gidan gaskiya bayan fama da gajeriyar rashin lafiya

- Ɗalibar mai suna, Mercy Sunday, ta mutu ne a safiyar ranar Talata kamar yadda ƙawarta ta faɗa

- Mai kula da al'amuran ɗalibai na BUK, Shamsudden Umar, ya tabbatar da faruwar lamarin

Wata ɗaliba ɗake shekarar ƙarshe a karatun kimiyyar siyasa a jami'ar Bayero Kano (BUK) ta rigamu gidan gaskiya ranar Talata a ɗakin kwanan ɗalibai na 'Ramat Hall', kamar yadda Punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: FG Ta Fito da Wani Sabon Tsari, Zata Tallafawa Yan Najeriya Miliyan Ɗaya da N5,000 na Tsawon Wata 6

Ɗalibar wacce aka bayyana sunan ta da, Mercy Sunday, ta mutu ne bayan zazzaɓi ya kama ta tare da amai, kamar yadda daily trust ta ruwaito.

Wata Ɗalibar Jami'ar BUK Ta Rigamu Gidan Gaskiya a Gidan Kwanan Ɗalibai
Wata Ɗalibar Jami'ar BUK Ta Rigamu Gidan Gaskiya a Gidan Kwanan Ɗalibai Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A cewar ƙawarta da suke ɗaki ɗaya wadda ta nemi a sakaya sunanta, tace Ms Sunday ta mutu ne da safiyar ranar Talata, jim kaɗan bayan wata kumfa ta fita daga bakin ta.

Mai kula da al'amuran ɗalibai na jami'ar BUK, Shamsuddeen Umar, ya tabbatar da mutuwar ɗalibar, yace ta mutu ne saboda lokacinta yayi.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: FG Ta Yi Ƙarin Haske Kan N-Power, Tace Mutum 550,000 Ne Suka Tsallake Matakin Tantancewa

Yace: "Bata da lafiya kuma taje asibitin makaranta, inda aka bata kulawa kuma daga baya aka sallameta, ta koma ɗakin kwanan dalibai."

Dr. Umar yace ciwon ta ya tashi a daren ranar Litinin, kuma akai rashin sa'a ta mutu kafin wayewar garin Talata.

A halin yanzun, an kai gawarta ɗakin ajiye gawarwaki kafin makusantanta su zo su ɗauke ta domin ayi mata jana'iza.

A wani labarin kuma Bayan Ganawa da Buhari, Gwamna Ya Bayyana Shirin Wasu Gwamnonin Ƙasar Nan Kafin Zaɓen 2023

Gwamnan Imo, Hope Uzodimma, ya bayyana cewa akwai gwamnonin ƙasar nan da dama da zasu koma APC.

Gwamnan yace duk da kalubalen da ake fuskan a wannan mulkin yana da yaƙinin APC zata lashe zaɓen 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel