Rashin tsaro: Ohanaeze ta bukaci Buhari da gwamnonin kudu maso gabas su kawo karshen kashe-kashe

Rashin tsaro: Ohanaeze ta bukaci Buhari da gwamnonin kudu maso gabas su kawo karshen kashe-kashe

- Kungiyar Ohaneze Ndigbo reshen jihohin arewa 19 da babban birnin tarayya sun yi tir da rashin tsaro a yankin kudu maso gabas

- Ohanaeze ta bukaci Shugaba Buhari da gwamnonin kudu maso gabas da su kawo karshen kashe-kashe da ke faruwa a yankin

- Ta kuma mika ta'aziyya da jaje ga iyalan wadanda suka rasa ransu sakamakon rashin tsaro

Kungiyar Ohaneze Ndigbo a jihohin arewa 19 da babban birnin tarayya sun yi Allah wadai da kashe-kashe da rashin tsaro a yankin Kudu maso Gabas.

Kungiyar ta kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da gwamnonin kudu maso gabas da su yi duk abin da ikonsu ya ba su na tsarin mulki don kawo karshen kashe-kashen da kare rayukan ’yan Najeriya, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: 'Yan kasuwar Arewa suna barazanar yanke hanyar samar da abinci a kasa baki daya

Rashin tsaro: Ohanaeze ta bukaci Buhari da gwamnonin kudu maso gabas su kawo karshen kashe-kashe
Rashin tsaro: Ohanaeze ta bukaci Buhari da gwamnonin kudu maso gabas su kawo karshen kashe-kashe Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Shugaban kungiyar, Barista Augustine Chimezie Amaechi, a cikin wata sanarwa a ranar Talata a Abuja ya kuma yi Allah wadai da kisan Ahmed Gulak, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a Owerri, yayin da ya ziyarci Imo.

Amaechi ya nuna damuwa kan karuwar rashin tsaro a kudu maso gabashin kasar yana mai cewa ba za a yarda da shi ba.

“Mun yi Allah wadai da kashe-kashe da barnata dukiyoyin gwamnati da aka yi a kudu maso gabas sannan muna jajantawa dangin wadanda suka rasa rayukansu. Muna kira ga hukumomin tsaro da su kaddamar da bincike don zakulo wadanda suka aikata wannan mummunan aiki tare da sanya su fuskantar doka.
“Don haka muna umartar Shugaban kasa, gwamnonin kudu maso gabas da su tabbatar da tsaron‘ yan Najeriya tare da kawo karshen wannan kashe-kashen saboda babu wanda ke da ‘yancin karbar rai sai da doka, abin da ke faruwa a yankin na kudu maso gabas abin tir ne, ba za a yarda da shi ba kuma bama goyon bayan shi," in ji shi.

Ya caccaki gwamnonin kudu maso gabas kan rashin sanin yakamata da kuma rashin karfin gwiwa don tunkarar matsalar tsaro a cewarsu lamarin da ya haifar da karuwar rashin tsaro a yankin.

Ya umarci gwamnonin da su tashi tsaye sannan su kare mutanen da aka zabe su don karewa.

Dangane da batun ballewa daga kabilu daban-daban, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta tattauna da su da nufin magance korafe-korafensu, inda ya kara da cewa zaman lafiya ya fi yaki.

KU KARANTA KUMA: Sojojin Najeriya sun dakile harin Boko Haram a Dikwa, jihar Borno

Rashin tsaro: A karshe kungiyar Ohanaeze ta yarda zata gana da dattawan Arewa

A gefe guda, kungiyar koli ta zamantakewar al’umman Ibo, Ohanaeze Ndigbo, ta yanke shawarar tattaunawa da shugabannin arewa kan yadda za a kame mummunan halin da ake ciki.

Jaridar The Sun ta ruwaito kawai cewa shugaban majalisar dattawan Ohaneze Ndigbo, Cif Emmanuel Iwuanyanwu, ya bayyana cewa yana kokari hada taron dattawan daga shiyyoyin biyu don tsara yadda za a magance matsalolin.

Legit.ng ta tattaro cewa Iwuanyanwu ya bayyana abubuwan da ke faruwa a kasar a matsayin masu matukar girgiza kuma gaba daya ya zarta yadda ake tsammani da tunanin dan adam.

Asali: Legit.ng

Online view pixel