Sojojin Najeriya sun dakile harin Boko Haram a Dikwa, jihar Borno

Sojojin Najeriya sun dakile harin Boko Haram a Dikwa, jihar Borno

- Dakarun rundunar Sojojin Najeriya ta yi nasarar dakile harin mayakan ISWAP a garin Dikwa da ke jihar Borno

- An tattaro cewa maharan a yammacin ranar Talata, sun kai mamaya garin cikin jerin gwano

- An kashe da yawa daga cikin maharan yayinda suka yi musayar wuta da sojin

Sojojin Najeriya sun yi nasarar dakile wani hari da aka kaiwa Dikwa, wani gari a jihar Borno, da yammacin Talata, PRNigeria ta ruwaito.

Jaridar ta bayar da rahoton cewa, dimbin ‘yan ta’adda dauke da muggan makamai, wadanda ake zargin ‘yan kungiyar aware ta Boko Haram ne, ISWAP, sun mamaye garin a cikin jerin gwanon motocin bindiga.

KU KARANTA KUMA: Waiwaye: Hotunan marigayiya matar Buhari, dalilin da yasa ya saki matarsa ta farko da wasu abubuwa 5

Sojojin Najeriya sun dakile harin Boko Haram a Dikwa, jihar Borno
Sojojin Najeriya sun dakile harin Boko Haram a Dikwa, jihar Borno Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Sai dai dakarun Sojojin Najeriya da na Rundunar Sojan Sama sun fatattaki 'yan ta'addan tare da dakile shirin na su, kafar watsa labaran ta ruwaito daga wata majiyar tsaro.

Majiyar ta ce an yi musayar wuta tsakanin sojojin Najeriya da ‘yan ta’adda tare da kashe da yawa daga cikin maharan.

Jaridar Premium Times ta nakalto majiyar tsaron tana cewa:

”An far wa‘ yan ta’addan da karfin tsiya. Wadanda suka tsira daga farmakin sojojin sun gudu, inda suka yi watsi da mummunan nufinsu.”

Dikwa na daya daga cikin garurwan Borno da suka sha fama da hare-hare daga kungiyar Boko Haram, wacce tuni ta rabe zuwa bangarori biyu.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: 'Yan kasuwar Arewa suna barazanar yanke hanyar samar da abinci a kasa baki daya

Jami'an tsaro sun lalata sansanin IPOB a Imo, sun ceto wata, sun kwato bindigogi

A wani labarin kuma, Jami'an tsaro na soji, 'yan sanda da sojin sama sun lalata daya daga cikin sansanonin kungiyar tsaro ta Gabas da ke da alaka da 'yan asalin yankin Biafra, Punch ta ruwaito.

Lalacewar ta afku ne a Amii-Akabo, da ke karamar hukumar Ikeduru ta jihar, biyo bayan kashe shugaban kungiyar ‘yan bindiga a jihar, wanda aka fi sani da Dragon.

Majiyar ‘yan sanda ta shaida cewa daya daga cikin 'yan kungiyar, Osinachi Stanley, ya jagoranci sojoji zuwa sansanin inda aka ceto wata mata ’yar sanda mai mukamin sufeto da ke tsare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng