Rashin tsaro: 'Yan kasuwar Arewa suna barazanar yanke hanyar samar da abinci a kasa baki daya

Rashin tsaro: 'Yan kasuwar Arewa suna barazanar yanke hanyar samar da abinci a kasa baki daya

- Karancin abinci na iya kunno kai a duk fadin kasar yayin da ‘yan kasuwar abinci na arewa suka yi barazanar shiga yajin aiki

- A cewar 'yan kasuwar, yarjejeniyar da suka yi da gwamnati a baya ba ta cika ba kuma batutuwan da aka gabatar a baya har yanzu suna ci gaba

- Yan kasuwar sun yi yajin aiki a baya sanadiyyar harin da aka kaiwa wasu mambobin su a yankin kudancin kasar

Yan kasuwar Arewa masu sayar da abinci karkashin inuwar kungiyar hadahadar kayan abinci da dillalan shanu a Najeriya (AUFCDN) sun yi barazanar sake komawa yajin aikin su tare da katse hanyar samar da abinci a duk fadin kasar.

Kungiyar ta ce za ta dauki matakin ne saboda gazawar gwamnatin tarayya na biyan diyyar naira biliyan 4.75 da ta amince da su.

KU KARANTA KUMA: Tsoffin shugabannin Najeriya, Obasanjo, Abdulsalami, da sauransu za su gana kan matsalolin da ke addabar kasar

Rashin tsaro: 'Yan kasuwar Arewa suna barazanar yanke hanyar samar da abinci a kasa baki daya
Rashin tsaro: 'Yan kasuwar Arewa suna barazanar yanke hanyar samar da abinci a kasa baki daya Hoto: Adekunle Ajayi/NurPhoto
Asali: Getty Images

‘Yan kasuwar, sun ba gwamnati wa’adin makonni uku don aiwatar da yarjejeniyar da aka sanya hannu wanda ya kai ga janye yajin aikinsu a watan Maris na bana.

Kungiyar ta yi zargin cewa har yanzu hukumomin tsaro suna karbar kudade daga mambobinta kuma suna musguna musu a yankin kudu maso gabas.

Da yake jawabi ga ‘yan jarida a ranar Talata, 8 ga watan Yuni, shugaban AUFCDN, Kwamared Muhammad Tahir, ya ce watanni uku bayan kungiyar ta dakatar da yajin aikin, har yanzu gwamnati ba ta biya musu bukatunsu ba.

Ya ce a lokacin da wa'adin makonni ukun ya kare, 'yan kasuwar za su tabbatar da toshe hanyoyin samar da abinci a duk fadin kasar.

Jaridar The Nation ta nakalto shi yana cewa:

“Mun amince da ci gaba da yajin aikinmu. Mun aika dukkan takardunmu a matsayin tuni ga shugabancin Majalisar kasa, IG na 'yan sanda, da dukkan hukumomin tsaro. Za mu jira mu ga me gwamnati za ta ce. Idan gwamnati ta kira mu game da batun to za mu dakatar da aiki.
“Ba mu kira yajin aiki ba. Muna jiran gwamnati don wannan tunatarwar. Za mu jira gwamnati daga yanzu zuwa makonni biyu-uku game da yarjejeniyar da ta sanya muka dakatar da yajin aikinmu. Tun da muka janye shi ba abin da aka yi.”

KU KARANTA KUMA: Arewa ke haifar da rashin tsaro a Kudu maso Gabas, Ohanaeze ta mayar da martani ga Wamakko

A halin yanzu, masana sun yi gargadin cewa abinci mara kyau na haifar da mutuwar mutum 420,000da basu kai ba a duniya.

A cewar jaridar The Guardian, Hukumar Abincin da Noma ce ta bayar da bayanan, tana mai gargadin cewa lafiyar abinci harkar kowa ce.

A wani labarin, Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmed Sani Yariman Bakura ya ce zai cigaba daga inda Muhammadu Buhari ya tsaya, idan har ya samu mulki.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Talata, 8 ga watan Yuni, 2021, ta ce Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura ya na neman zama shugaban kasa.

Ahmed Sani Yariman Bakura ya yi alkawari idan har aka zabe shi a 2023, zai cigaba daga manfufofin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng