Bayan Ganawa da Buhari, Gwamna Ya Bayyana Shirin Wasu Gwamnonin Ƙasar Nan Kafin Zaɓen 2023

Bayan Ganawa da Buhari, Gwamna Ya Bayyana Shirin Wasu Gwamnonin Ƙasar Nan Kafin Zaɓen 2023

- Gwamnan Imo, Hope Uzodimma, ya bayyana cewa akwai gwamnonin ƙasar nan da dama da zasu koma APC

- Gwamnan yace duk da kalubalen da ake fuskan a wannan mulkin yana da yaƙinin APC zata lashe zaɓen 2023

- Yace akwai wasu tsirarun mutane dake ƙoƙarin ganin sun kai wannan gwamnatin ƙasa

Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo, yayi hasashen cewa APC zata samu nasara a zaɓen 2023 duk kuwa da ƙalubalen tsaron da ake fama dashi a mulkinta, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: FG Ta Yi Ƙarin Haske Kan N-Power, Tace Mutum 550,000 Ne Suka Tsallake Matakin Tantancewa

Uzodimma yayi wannan hasashe ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a fadar shugaban ƙasa jim kaɗan bayan fitowa daga ganawar sirri da shugaba Buhari.

Gwamnan yace akwai gwamnoni da dama a ƙasar nan da zasu sauya sheka zuwa APC kafin zaɓen 2023.

Bayan Sa Labule da Buhari, Gwamna Ya Bayyana Shirin Wasu Gwamnonin Ƙasar Nan Kafin Zaɓen 2023
Bayan Sa Labule da Buhari, Gwamna Ya Bayyana Shirin Wasu Gwamnonin Ƙasar Nan Kafin Zaɓen 2023 Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A cewarsa, gwamnonin sun fahimci akwai wasu tsirarun mutane dake ƙoƙarin kai wannan gwamnatin ƙasa saboda wata buƙatar kansu.

Da aka tambayeshi ko akwai wasu gwamnoni da zasu sauya sheƙa zuwa APC a yankin kudu maso gabas, gwamnan yace:

"Ba wai daga yankin kudu-gabas ba kaɗai ba, gwamnonin ƙasar nan da dama zasu dawo APC. Kunga dai abunda ya faru kwanan nan,."

"Matsalar wannan gwamnatin shine akwai wasu tsirarun mutane dake son ganin bayanta."

KARANTA ANAN: Wani Kwamishina Ya Rasa Muƙaminsa Saboda Yaƙi Bin Gwamna Zuwa APC

"Saboda babu wanda ya taɓa faɗa mun cewa wannan gwamnatin ba ta yin aiki, misali ace ba ta biyan albashi, ba ta gina hanyoyin mota, aikin titin jirgin ƙasa baya tafiya ko wasu abubuwan."

"Babu wanda keda wata sahihiyar hanya da zai soki wannan gwamnatin. Sai dai kaji ana cewa tsakanin makiyaya da manoma ana faɗa, sabida haka an sace mutum 200." inji gwamnan.

A wani labarin kuma an bayanna Sunayen Wasu Makusantan Shugaba Buhari da Suka Bijire Wa Umarninsa Na Hana Amfani da Twitter

Bayan gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwar hana amfani da twitter, an samu wasu jigogin gwamnatin sun bijirewa dokar, kamar yadda bbc hausa ta ruwaito.

Rahotanni sun tabbatar da cewa har yanzun yan Najeriya na amfani da shafin twitter ta hanyar amfani da manhajar VPN.

Asali: Legit.ng

Online view pixel