Tsoffin shugabannin Najeriya, Obasanjo, Abdulsalami, da sauransu za su gana kan matsalolin da ke addabar kasar

Tsoffin shugabannin Najeriya, Obasanjo, Abdulsalami, da sauransu za su gana kan matsalolin da ke addabar kasar

- A tsaka da dimbin kalubalen da Najeriya ke fuskanta, wasu shugabannin Najeriya sun kira muhimmin taro

- Tsohon shugaban kasa Obasanjo da tsohon shugaban kasa a mulkin soja Abdulsalami Abubakar suna daga cikin wadanda ake sa ran za su halarci taron

- Za a tattauna muhimman batutuwa kamar hadin kan kasa da tsaro a taron da aka shirya gudanarwa a ranar Alhamis, 10 ga watan Yuni

Kungiyar hadin kan mabiya addinai daban-daban don samar da zaman lafiya ta kira taro don tattaunawa kan "lamuran da suka shafi kasar".

A cewar jaridar The Cable, kungiyar tana karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Sa’ad Abubakar, Sarkin Musulmi; Abdulsalami Abubakar, tsohon shugaban kasa, da John Onaiyekan, tsohon babban bishop din Katolika na Abuja.

KU KARANTA KUMA: Arewa ke haifar da rashin tsaro a Kudu maso Gabas, Ohanaeze ta mayar da martani ga Wamakko

Tsoffin shugabannin Najeriya, Obasanjo, Abdulsalami, da sauransu za su gana kan matsalolin da ke addabar kasar
Tsoffin shugabannin Najeriya, Obasanjo, Abdulsalami, da sauransu za su gana kan matsalolin da ke addabar kasar Hoto: ISSOUF SANOGO/AFP, PIUS UTOMI EKPEI/AFP, TONY KARUMBA/AFP
Asali: Getty Images

Legit.ng ta tattaro cewa an shirya gudanar da taron ne a ranar 10 ga watan Yuni, a Transcorp Hilton da ke Abuja.

Batutuwan da za a tattauna a taron sun hada da na hadin kan kasa, tsaro, zaman lafiya, hadewa, farfado da tattalin arziki, da ci gaba, A cewar Sahara Reporters.

An tattaro cewa shugaban kungiyar kwadagon Najeriya (NLC), Ayuba Wabba, na daya daga cikin masu ruwa da tsaki da aka gayyata taron.

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin kudu yan wasan barkwanci ne – Kungiyar Miyetti Allah

Lamarin Najeriya sai Allah, ku mika kukanku gareshi Obasanjo ga 'yan Najeriya

A baya tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi koka wa Allah domin magance matsalar tsaro da ta mamaye kasar nan, TheCable ta ruwaito.

Ya yi wannan magana ne a ranar Asabar a Abeokuta, jihar Ogun, yayin bikin karin kumallo karo na 16 wanda kungiyar kiristocin Najeriya (CAN), reshen jihar Ogun ta shirya don karrama shi.

Obasanjo ya ce kalubalen da ke gaban Najeriya ya wuce abin da ‘yan kasa da shugabannin za su iya dauka, amma ba su karfin Allah ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng