Lamarin Najeriya sai Allah, ku mika kukanku gareshi Obasanjo ga 'yan Najeriya
- Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya yi kira ga 'yan Najeriya su koma ga Allah duba da matsalolin kasar
- Ya bayyana cewa, matsalolin Najeriya sun fi karfin kasar, amma ba su karfin Allah ba ko kadan
- Ya ce ya kamata 'yan Najeriya su koka damuwarsu ga Allah domin samun mafita ga kasar a yanzu
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi koka wa Allah domin magance matsalar tsaro da ta mamaye kasar nan, TheCable ta ruwaito.
Ya yi wannan magana ne a ranar Asabar a Abeokuta, jihar Ogun, yayin bikin karin kumallo karo na 16 wanda kungiyar kiristocin Najeriya (CAN), reshen jihar Ogun ta shirya don karrama shi.
Obasanjo ya ce kalubalen da ke gaban Najeriya ya wuce abin da ‘yan kasa da shugabannin za su iya dauka, amma ba su karfin Allah ba.
KU KARANTA: Rikici ya kai ga sojoji kashe jami'in tsaron farin kasa na DSS a cikin wani otal
Ya nanata mahimmancin addu’o’i wajen magance matsaloli, ya kara da cewa Najeriya na bukatar warkarwa daga Allah.
"Halin da ake ciki a kasarmu na bukatar dukkaninmu da mu yi kuka ga Allah cikin addu'oi da roko," in ji shi.
“Da alama mun cika da rashin sanin yadda za mu magance rikicin kasar mu. Amma babu abin da ya fi karfin Allah. Wannan shine dalilin da yasa muke nan. Muna da kalubale. Wadannan sun fi karfin abin da za mu iya dauka. Dole ne mu yi kuka ga Allah don ya taimake mu.
“Kasar mu na bukatar warkewa. An fi karfinmu, wadanda suke cikin gwamnati, masu zartarwa, ‘yan majalisa, ma’aikatan gwamnati, kamfanoni masu zaman kansu, abin ya wuce karfinmu.
Da yake magana daga littafin Zabura sura 27 aya 7, tsohon Shugaban ya yi magana kan bukatar addu’o’i don shawo kan matsalolin da kasar ke fama da su a halin yanzu, The Nation ta ruwaito.
KU KARANTA: An dakile harin 'yan ta'adda a hedkwatar 'yan sanda ta Imo, an hallaka tsageru 5
A wani labarin, Wani tsohon hadimin Shugaba Buhari, kan lamuran Majalisa, Abdurrahman Sumaila, ya ce ‘yan Najeriya masu tunani ba za su jefa rayukansu cikin hadari ba don mara wa takarar duk wani dan siyasar Kudu maso Gabas da ke neman shugabancin kasar nan a 2023 ba.
Sumaila ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kano ranar Alhamis, jaridar Punch ta ruwaito.
“Tare da wadannan munanan dabi’un da mutanen Kudu-maso-Gabas suka aikata, ta yaya 'yan Najeriya za su ba su amanar su shugabance mu?
Asali: Legit.ng