Sunayen Wasu Makusantan Shugaba Buhari da Suka Bijire Wa Umarninsa Na Hana Amfani da Twitter

Sunayen Wasu Makusantan Shugaba Buhari da Suka Bijire Wa Umarninsa Na Hana Amfani da Twitter

- Bayan gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwar hana amfani da twitter, an samu wasu jigogin gwamnatin sun bijirewa dokar

- Rahotanni sun tabbatar da cewa har yanzun yan Najeriya na amfani da shafin twitter ta hanyar amfani da manhajar VPN

- A ranar Jumu'a ne gwamnatin tarayya ta bayyana dokar hana hawa shafin kamar yadda ministan yaɗa labarai ya sanar

Bayan dakatarwar da gwamnatin shugaba Buhari ta yi wa kamfanin twitter a Najeriya, wasu jiga-jigan jam'iyyar APC kuma makusantan Buhari sun bijerewa umarnin shugaban inda suka sake yin amfani da shafin twitter.

KARANTA ANAN: Manyan Dalililai 5 da Suka Tabbatar da Mutuwar Shugaban Boko Haram, Abubakar Sheƙau

A ranar jumu'a da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwar cewa ta dakatar da amfani da twitter a faɗin ƙasar bayan kamfanin ya goge rubutun da shugaba Buhari yayi.

Rahoton BBC ya bayyana wasu makusantan shugaba Buhari da suka karya wannan doka ta hanyar yin amfani da shafin twitter.

Sunayen Wasu Makusantan Shugaba Buhari da Suka Bijire Wa Umarninsa Na Hana Amfani da Twitter
Sunayen Wasu Makusantan Shugaba Buhari da Suka Bijire Wa Umarninsa Na Hana Amfani da Twitter Hoto: bbc.com
Asali: UGC

1. Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i.

Bayan sanarwar gwamnatin Buhari Ranar jumu'a, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, yayi wani sabon rubutu a shafinsa na twitter.

Gwamnan ya wallafa wata magana da kamfanin watsa labarai na Routers ya buga wanda ke cewa "Gwamnatin Najeriya ta nuna wa Amurka yadda zata tafiyar da manyan kafafen sada zumunta."

2. Gwamnan Oyo, Seyi Makinde.

Shima gwamnan Oyo, Makinde, yayi rubutu a shafinsa na twitter bayan dokar FG, inda ya bayyana damuwarsa kan harin da wasu yan bindiga suka kai garin Ingangan, jihar Oyo, ranar Lahadi.

KARANTA ANAN: Muhimman Hanyoyi 6 da Hana Amfani da Twitter Zai Shafi Yan Najeriya da Kasuwancinsu

3. Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Odunayo Akeredolu.

Gwamna Akeredolu, ya wallafa a shafinsa na twitter cewa sun umarci rundunar jami'an tsaron yankin kudu maso gabas ta kira taron kwamandojinta domin fara aikin dawo da zaman lafiya nan take.

4. Hukumar daƙile yaɗuwar cututtuka NCDC

Hukumar NCDC ta wallafa a shafinta na twitter rahoton gwajin cutar COVID19 da ta saba fitarwa a kullum da misalin ƙarfe 12:02 na daren ranar Asabar.

A wani labarin kuma NBC Ta Umarci Dukkan kafafen Watsa Labarai Su Dakatar da Amfani da Twitter

Hukumar NBC ta umarci dukkan tashoshin Radio, talabishin da su dakatar da amafani da twitter nan take

Wannan umarnin na zuwa ne biyo bayan dokar hana amfani da twitter a Najeriya da FG ta sanar ranar Jumu'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel