Babu Tantama APC Ce Zata Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a 2023, Inji Wani Jigo

Babu Tantama APC Ce Zata Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a 2023, Inji Wani Jigo

- Wani jigon jam'iyyar APC a jihar Delta kuma ɗan majalisar wakilai na tarayya yayi hasashen zaɓen shugaban ƙasa dake tafe

- Yace babu tantama APC mai Mulki ce zata sake ɗarewa kujerar shugabancin ƙasar nan, kuma PDP ta fara nuna damuwa da hakan

- Ya kuma yi kira da shugabannin APC musamman na mazabun da yake wakilta da su ƙara haɗan kansu

Jam'iyyar APC mai mulki ce zata sake ɗarewa kujerar shugabancin ƙasar nan a babban zaɓen 2023 mai zuwa a hasashen wani ɗan majalisar wakilai, Rev. Francis Ejiroghene Waive, daga jihar Delta, kamar yadda the nation ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Wasu Yan Bindiga Sun Hallaka Kwamandan Jami'an NSCDC a Abuja

Ɗan majalisar ya ƙara da cewa a halin yanzun babbar jam'iyyar hamayya PDP ta fara damuwa da wannan nasara da ake hange.

Babu Tantama APC Ce Zata Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a 2023, Inji Wani Jigo
Babu Tantama APC Ce Zata Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a 2023, Inji Wani Jigo Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Waive ya faɗi haka ne yayin wata ziyara da yakai wa jigon jam'iyyar, Olorogun Ogbarode Ogbon, a garin Effurun, ƙaramar hukumar Uvwie, jihar Delta.

Waive yana wakiltar mazaɓun Ugheli ta arewa, Ugheli ta kudu da Udu a majalisar wakilan tarayya ƙarƙashin jam'iyyar APC.

Da yake jaddada buƙatar haɗin kai tsakanin shugabannin APC a faɗin jihar, musamman a ƙaramar hukumar Ugheli ta kudu, Waive ya roƙe su da su ƙara fahintar juna tare da haɗa kan su.

KARANTA ANAN: Karin Bayani: Shugaba Buhari Ya Gana da Sabon Hafsan Sojin Ƙasa, Manjo Janar Farouk Yahaya

Ɗan majalisar ya ƙara da cewa shugaban APC na jihar, Olorogun O’tega Emerhor, ya gina jagoranci mai kyau wanda ya haɗa mutane wuri ɗaya kuma a kan gaskiya.

Yace: "Ɗaya daga cikin shawarwarin da nake bayarwa a mazaɓu na itace, kar mu sake mu raba kanmu, kada wani abu yasa kowa ya kama ɓangare daban."

"Ƙaramar hukumar Ugheli ta kudu na ɗaya daga cikin inda PDP ke taƙama da su, amma zamu canza wannan tarihin, kuma zamu iya."

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Jagoranci Sake Buɗe Makarantar Chibok, Ya Canza Mata Sabon Suna

Shugaban Ƙasa Buhari ya ƙaddamar da sabuwar makarantar Chibok da aka sake ginawa kuma aka canza mata suna, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Shugaban wanda ministan mata, Mrs Pauline Tallen, ta wakilta, yace gwamnatinsa na iya ƙoƙarinta wajen ganin komai ya daidaita a garin Chibok.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262