Muhimman Hanyoyi 6 da Hana Amfani da Twitter Zai Shafi Yan Najeriya da Kasuwancinsu

Muhimman Hanyoyi 6 da Hana Amfani da Twitter Zai Shafi Yan Najeriya da Kasuwancinsu

- Yan Najeriya na amfani kafar sada zumunta na twitter a ɓangarorin rayuwarsu masu muhimmanci

- Wannan rahoton zai tattaro muku muhimman abubuwa 6 da hana hawa twitter zai jawo wa ɗan Najeriya

- A ranar jumu'a da ta gabata ne, gwamnatin Najeriya ta sanar da dakatar da amfani da shafin twitter

Sama da shekaru 10 da suka wuce, twitter ya kasance ɗaya daga cikin kafafen sada zumunta da suka fi shahara wajen samu labarai da sauran al'amuran rayuwa.

KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 26 a Wani Mummunan Hari a Jihar Zamfara

A ranar jumu'a ta gabata gwamtanin tarayya ta sanar da dakatar da twitter a faɗin ƙasar, Najeriya itace ƙasar da tafi kowace kasa yawan al'umma a nahiyar Africa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Legit.ng hausa ta tattaro muku Hanyoyi 6 da hana amfani da twitter zai shafi yan Najeriya da kasuwancin su.

1. Tattaunawar kaduwanci.

Yan Najeriya da dama masu kananan kasuwanci suna amfani da shafin twitter wajen tallata hajar su. Duk da suna amfani da sauran kafafe kamar Instagram, Facebook da sauransu.

Manyan yan kasuwa na amfa da shafin twitter wajen sanar da kwastomominsu cewa sun kawo sabbin kaya.

Jerin Hanyoyi 6 da Hana Amfani da Twitter Zai Shafi Yan Najeriya da Kasuwancinsu
Jerin Hanyoyi 6 da Hana Amfani da Twitter Zai Shafi Yan Najeriya da Kasuwancinsu Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

2. Damar samun aikin yi.

Yan Najeriya da dama na samun aikin yi ta hanyar amfani da twittter, hana amfani da shafin zai dakatar da samun wannan damar ga yan Najeriya.

3. Damar nuna kai.

Mutanen da basu da yawa, musamman ƙananan ƙalbilu na amfani da twitter wajen bayyana kansu. Hakanan kuma yan Najeriya na amfani da shafin domin nuna ainihin abubuwan dake faruwa dasu a yankunan su.

4. Labarai.

Yan Najeriya na amfani da twitter wajen samun labarai, jaridu talabishin da Radio duk suna amfani da shafin wajen watsa labaran su.

KARANTA ANAN: Murna Ta Koma Ciki: Hatsari Ya Laƙume Rayukan Matasa 17 Akan Hanyar Dawowa Daga Ɗaurin Aure

5. Koyon ilimin rayuwa.

Twitter shafi ne mai kyau da zaka koyi abubuwa da dama da baka sani ba. Misali, a twitter zaka haɗu da mutane daban-daban yan ƙabilu daban-daban.

6. Neman taimakon kuɗi don yin wani muhimmin abu.

Yayin da tattalin arziƙin Najeriya yake ƙara faɗuwa, yan Najeriya da dama na amfani da twitter wajen taimakawa junansu a ɓangaren lafiya, ilimi da kuma gudanar da rayuwar yau da kullum.

A lokaci da dama zakaga yan Najeriya sun taimaka sosai domin fitar da wani daga cikin wani ƙangin rayuwa da ya shiga.

A wani labarin kuma An Tsinci Gawar Ɗaya Daga Cikin Ɗaliban Islamiyya da Yan Bindiga Suka Sace a Neja

An gano gawar ɗaya daga cikin ɗaliban da aka sace a islamiyyar garin Tegina, jihar Neja, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa an tsinci gawar yaron ɗan shekara uku kacal a bayan garin Tegina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel