Da Ɗumi-Ɗumi: NBC Ta Umarci Dukkan Tashoshin Watsa Labarai Su Dakatar da Amfani da Twitter

Da Ɗumi-Ɗumi: NBC Ta Umarci Dukkan Tashoshin Watsa Labarai Su Dakatar da Amfani da Twitter

- Hukumar NBC ta umarci dukkan tashoshin Radio, talabishin da su dakatar da amafani da twitter nan take

- Wannan umarnin na zuwa ne biyo bayan dokar hana amfani da twitter a Najeriya da FG ta sanar ranar Jumu'a

- Sai dai har yanzun akwai wasu yan Najeriya dake amfani da twitter ta hanyar amfani da manhajar VPN

Hukumar kula da tashoshin watsa labarai ta ƙasa (NBC) ta umarci ɗaukacin tashoshin watsa labarai da su dakatar da amfani da dandalin sada zumunta na twitter, kamar yadda daily Nigerian ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Jerin Hanyoyi 6 da Hana Amfani da Twitter Zai Shafi Yan Najeriya da Kasuwancinsu

Wannan umarnin na ƙunshe ne a cikin jawabin da muƙaddashin darakta janar na NBC, Armstrong Idachaba, ya fitar a yau Litinin.

Wannan ya biyo bayan dakatar da kamfanin twitter da gwamnatin tarayya tayi ranar Jumu'a da ta gabata, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Da Ɗumi-Ɗumi: NBC Ta Umarci Dukkan Tashoshin Watsa Labarai Su Dakatar da Amfani da Twitter
Da Ɗumi-Ɗumi: NBC Ta Umarci Dukkan Tashoshin Watsa Labarai Su Dakatar da Amfani da Twitter Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Dakatarwan ta biyo bayan matakin da twitter ya ɗauka na goge rubutun da shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yayi.

Idachaba yace: "Kowa ce tashar watsa labarai ta cire twitter daga cikin tsarinta na haɗa labarai da kuma watsa shirye-shirye musamman na wayar salula."

"Dokar sashi na 2 (1) ta baiwa NBC dama kuma ta ɗora mata alhakin tabbatar da tashoshin watsa labarai na bin dokar ƙasa yadda ya kamata."

"Kusani duk wata tasha da ta cigaba da amfani da twitter da aka dakatar to ta saba wa dokar ƙasa, saboda haka muna buƙatar cikakken haɗin kai daga wurin ku."

KARANTA ANAN: Murna Ta Koma Ciki: Hatsari Ya Laƙume Rayukan Matasa 17 Akan Hanyar Dawowa Daga Ɗaurin Aure

Legit.ng hausa ta gano cewa har yanzun akwai yan Najeriya dake amfani da twitter ta hanyar amfani da manhajar (VPN).

A wani labarin kuma Nan Gaba Ƙaɗan Wasu Gwamnonin PDP Zasu Sauya Sheƙa Zuwa APC, Ganduje

Gwamnan Kano , Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa nan gaba kaɗan APC zata yi sabbin gwamnoni daga jam'iyyar PDP.

Gwamna Ganduje yace tuni jam'iyya mai mulki ta fara shirye- shiryen tarbar gwamnonin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel