Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 33, Sun Yi Awon Gaba da Dabbobi da Dama a Kaduna da Zamfara

Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 33, Sun Yi Awon Gaba da Dabbobi da Dama a Kaduna da Zamfara

- Yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 33 a wasu hare-hare da suka kai jihohin Zamfara da Kaduna

- Yan bindigan sun kashe mutum 30 a ƙauyukan Askawa da Gidan Danunu, Jihar Zamfara

- A kaduna kuma, Wasu yan ta'adda na daban da sojoji suka koro sun kashe mutum uku, cikin su harda fasinja

Yan bindiga sun hallaka aƙalla mutum 33 a wasu jerin hare-hare da suka kai jihohin Kaduna da Zamfara, kamar yadda the nation ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Wasu Yan Bindiga Sun Hallaka Kwamandan Jami'an NSCDC a Abuja

An kashe mutum 30 a wani hari da aka kai ƙauyen Askawa da Gidan Danunu dake ƙaramar hukumar Zumu, jihar Zamfara.

Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 33, Sun Yi Awon Gaba da Dabbobi da Dama a Kaduna da Zamfara
Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 33, Sun Yi Awon Gaba da Dabbobi da Dama a Kaduna da Zamfara Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

A jihar Kaduna, wasu yan bindiga dake shirin kai hari wani ƙauye sun gamu da dakarun soji, inda suka fatattake su, amma duk da haka saida yan ta'addan suka kashe mutum uku.

Bataliyar sojin ƙasa na 4Demo sune suka samu nasarar fafatawa da maharan har suka kore su.

Kwamishinan tsaro da al'amuran cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, shine ya bayyana haka a wani saƙo da ya fitar.

KARANTA ANAN: Babu Tantama APC Ce Zata Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a 2023, Inji Wani Jigo

Yace maharan sun kashe wani fasinja a babbar hanyar Zaria-Kaduna, wanda har yanzun ba'a gano asalin inda ya fito ba.

Mr. Aruwan yace dakarun sojin sun kawo wa gwamnati rahoton cewa sun samu nasarar fatattakar wasu yan bindiga a wani wuri dake kan hanyar Zaria-Kaduna.

Yace: "Yan bindigan, waɗanda jami'an soji suka kora, sun canza hanya, inda anan ne suka farmaki ƙauyen Dunki, kuma suka kashe mutum biyu, Abubakar Sani da Abubakar Saleh."

"Hakanan kuma sun harbe wani fasinja har lahira, wanda a halin yanzun bamu gano ko ɗan wane gari bane."

Kwamishinan ya ƙara da cewa maharan sun shiga ƙauyukan Mashashiya da Farguza, inda suka yi awon gaba da dabbobin kiwo.

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Gana da Sabon Hafsan Sojin Ƙasa, Manjo Janar Farouk Yahaya

Shugaba Buhari ya gana da sabon hafsan sojin ƙasa, Manjo Janar Farouk Yahaya a fadarsa dake Abuja

Wannan shine karon farko da shugaban yake ganawa da COAS ɗin tun bayan naɗa shi a wannan matsayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel