Wasu Yan Bindiga Sun Hallaka Kwamandan Jami'an NSCDC a Abuja

Wasu Yan Bindiga Sun Hallaka Kwamandan Jami'an NSCDC a Abuja

- Wasu yan bindiga sun kashe ɗaya daga cikin kwamandojin hukumar NSCDC a Abuja

- Kakakin hukumar, Olusola Odumosu, shine ya bayyana haka a wurin ƙaddamar da tawagar mata

- Yace kwamandan ya samu raunukan harbi a yayin harin yan bindigan, inda daga baya ya rasu ranar Litinin da safe

Hukumar NSCDC ta ƙasa ta tabbatar da kashe kwamandan jami'anta na Abuja wanda yan bindiga suka yi a kan hanyar Kuje-Gwagwalada ranar Lahadi, kamar yadda the nation ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Karin Bayani: Shugaba Buhari Ya Gana da Sabon Hafsan Sojin Ƙasa, Manjo Janar Farouk Yahaya

Kwamandan wanda aka fi sani da 'Kwamanda Dangana' ya samu raunukan harbi a jikinsa yayin harin yan bindiga, daga baya ya mutu da safiyar Litinin.

Wasu Yan Bindiga Sun Hallaka Kwamandan Jami'an NSCDC a Abuja
Wasu Yan Bindiga Sun Hallaka Kwamandan Jami'an NSCDC a Abuja Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Anyi shiru na tsawon minti ɗaya domin girmamawa ga marigayin yayin wani fareti da jami'an NSCDC suka gudanar.

Jami'an sun yi fareti ne a wurin ƙaddamar da sabuwar tawagar mata ta hukumar da kuma filin faretin su a sakateriyar NSCDC dake Abuja.

KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Jagoranci Sake Buɗe Makarantar Chibok, Ya Canza Mata Sabon Suna

Kakakin NSCDC, Olusola Odumosu, wanda ya bayyana mutuwar kwamandan, yayi addu'a ga mamacin tare da sauran jami'ai.

Kwamanda Janar, Dr. Ahmed Audi, ya bayyana yanayin tsaron ƙasar nan a matsayin wani abun damuwa matuka.

Yace: "Jami'an hukumarsa na kan hanyar juya akalarsu domin su samu damar bada gudummuwar su wajen magance matsalar tsaro a ƙasar nan."

A wani labarin kuma Matan Gwamnoni Sun Yi Magana Kan Matsalar Tsaro, Rashin Aikin Yi, Da Talaucin da Yan Najeriya Suke Ciki

Matan gwamnonin ƙasar nan ƙaraƙashin ƙungiyar su sun bayyana matuƙar damuwar su kan karuwar matsalar tsaro a faɗin Najeriya tare da talaucin da ya addabi yan ƙasa.

Shugabar ƙungiyar, Bisi Fayemi, itace ta bayyana haka a Abuja , jim kaɗan bayan fitowa daga taron da suka gudanar, kamar yadda punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262