Karin Bayani: Shugaba Buhari Ya Gana da Sabon Hafsan Sojin Ƙasa, Manjo Janar Farouk Yahaya
- Shugaba Buhari ya gana da sabon hafsan sojin ƙasa, Manjo Janar Farouk Yahaya a fadarsa dake Abuja
- Wannan shine karon farko da shugaban yake ganawa da COAS ɗin tun bayan naɗa shi a wannan matsayi
- Yayin taron Buhari ya baiwa sabon shugaban sojiin shawarwari da kuma ƙarfin guiwa kan aikinsa
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya gana da sabon hafsan rundunar sojin ƙasa, Manjo Janar Farouk Yahaya, a fadarsa dake babban birnin tarayya Abuja.
KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Jagoranci Sake Buɗe Makarantar Chibok, Ya Canza Mata Sabon Suna
Wannan ganawa dai tazo kwanaki kaɗan bayan shugaban ya naɗa sabon hafsan sojin ƙasa biyo bayan mutuwar janar Ibrahim Attahiru.
Mai taimakawa shugaban kan harkokin yaɗa labarai, Bashir Ahmad, shine ya bayyana haka a wani rubutu da yayi a shafinsa na kafar sada zumuntar Facebook.
A yayin taron, shugaba Buhari yace akwai ƙalubale da dama da matsin lamba a ɓangaren tsaron ƙasar nan saboda haka akwai buƙatar jami'an tsaro su haɗa kan su.
KARANTA ANAN: Babbar Magana: FG Ta Gayyaci Jakadun Amurka, Burtaniya Kan Maganar da Sukayi Bayan Hana Amfani da Twitter
Ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi, wanda aka yi taron tare da shi, ya zanta da manema labarai bayan fitow daga taron cewa shugaba Buhari ya baiwa shugaban rundunar sojin shawarwari da kara masa ƙarfin guiwa.
Legit.ng hausa ta tattaro wasu daga cikin ra'ayoyin yan Najeriya akan wannan ganawar.
Muntaƙa Muhammad Sifawa yace:
"Ina rokon Allah ya taimake su, ya kare su a cikin wannan yanayi mai wahala domin su lalubo hanyar warware ƙalubalen tsaron da ƙasar mu ke fama da ita."
Ustaz Muhammad Jikan Ali yace:
"Mu dai ku taimaka ku samar mana da tsaro mu koma gona."
Abubakar Labaran Lmam yace:
"Allah yasa ku gama wannan taro lafiya."
Aliyu Salisu Ask yace:
"Ina addu'a Allah yasa albarka a wannan taron."
A wani labarin kuma NBC Ta Umarci Dukkan Tashoshin Watsa Labarai Su Dakatar da Amfani da Twitter
Hukumar NBC ta umarci dukkan tashoshin Radio, talabishin da su dakatar da amafani da twitter nan take.
Wannan umarnin na zuwa ne biyo bayan dokar hana amfani da twitter a Najeriya da FG ta sanar ranar Jumu'a.
Asali: Legit.ng