Badakalar Abacha: Makudan kudaden da Najeriya ta kwato cikin shekaru 23
Tsokacin Edita: Kamar yadda shugaba Buhari yake yawwan fadi: "Idan ba mu kashe cin hanci da rashawa ba, rashawa za ta kashe Najeriya," Najeriya na ci gaba da fuskantar almundahana daga jiga-jigan gwamnati. Najeriya ta kwato kudade da dama daga hannun iyalan tsohon shugaban ta na mulkin soja, Janar Sani Abacha.
Sani Abacha ya yi aiki a matsayin shugaban mulkin sojan Najeriya daga 1993 zuwa rasuwarsa a 1998. Sai dai, tun bayan rasuwarsa, Najeriya na ci gaba da dawo da biliyoyin nairorin da ya sata ya kai kasashe daban-daban wadanda a yanzu ake wa lakabi da 'Badakalar Abacha'.
Wannan rubutu ya tattaro "Badakalar Abacha" da aka kwato a karkashin gwamnatocin da suka gabata daga 1998 zuwa 2020, kamar yadda yazo a rahoton TheCable.
KU KARANTA: Zan karfafa muku cin naman Alade a madadin na Shanu, Akeredolu ga 'yan jiharsa
1. Abdulsalami Abubakar (Dala miliyan 750)
Abdulsalami Abubakar ya gaji Abacha a 1988 kuma ya sauya tsarin gwamnatin Najeriya zuwa dimokiradiyya a shekarar 1999.
A shekarar 1988, ya kwato dala miliyan 750 daga dangin Abacha.
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya mulki Najeriya daga shekarar 1999 zuwa 2007. A shekarar 2000, ya kwato dala miliyan 64 daga kasar Switzerland da Abacha ya boye.
A shekara ta 2002, Obasanjo ya dawo da dala biliyan 1.2 ta hanyar yarjejeniya da dangin Abacha.
A shekarar 2003, tsohon shugaban ya kuma kwato dala miliyan 160 daga Jersey, British Island da dala 88 daga Switzerland.
Obasanjo ya kuma kwato dala miliyan 461 daga Switzerland a 2005 da dala miliyan 44 daga kasar a 2006.
3. Goodluck Jonathan
A shekarar 2014, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kwato dala miliyan 227 daga Liechtenstein.
4. Muhammadu Buhari
A shekarar 2018, Shugaba Muhammadu Buhari ya kwato dala miliyan 322 daga Switzerland yayin da a shekarar 2020, ya kwato dala miliyan 308 daga Jersey / USA.
Adadin kudin da aka kwato ya zuwa yanzu ya kusan dala biliyan 3.624.
KU KARANTA: El-Rufa'i da wani gwamnan APC sun bijirewa umarnin Buhari na hana Twitter
A wani labarin, Wani tsohon hadimin Shugaba Buhari, kan lamuran Majalisa, Abdurrahman Sumaila, ya ce ‘yan Najeriya masu tunani ba za su jefa rayukansu cikin hadari ba don mara wa takarar duk wani dan siyasar Kudu maso Gabas da ke neman shugabancin kasar nan a 2023 ba.
Sumaila ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kano ranar Alhamis, jaridar Punch ta ruwaito.
“Tare da wadannan munanan dabi’un da mutanen Kudu-maso-Gabas suka aikata, ta yaya 'yan Najeriya za su ba su amanar su shugabance mu?
Asali: Legit.ng