Lai Mohammed ya caccaki masu lalata kadarorin gwamnati, ya ce 'yan ta'adda ne

Lai Mohammed ya caccaki masu lalata kadarorin gwamnati, ya ce 'yan ta'adda ne

-Ministan yada labarai a Najeriya ya koka kan yawaitar lalata kayayyakin gwamnati a kasar

- Ya ce, masu kone ofisoshin INEC da sauran kadarorin gwamnati lallai 'yan ta'adda ne a kasar

- Ya bayyana haka ne a wani taron da ya samu halartar wasu ministoci da jiga-jigan gwamnati

Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed a ranar Litinin ya bayyana rusa ofisoshin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, ofisoshin 'yan sanda da sauran kayayyakin jama'a a matsayin aikin ta'addanci, Daily Trust ta ruwaito.

Da yake magana a Abuja a wani taro kan kare abubuwan more rayuwar jama'a, ya ce ana lalatawa tare da sace abubuwan hanyoyin jirgin kasa, layukan dogo, fitilun kan titi da sauran kayayyakin wutar lantarki, bututun mai, kayayyakin sadarwa da kayayyakin jirgin sama a kasar.

Taron ya samu halartar Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Raji Fashola, SAN; takwaransa na Sufuri, Rotimi Amaechi; Ministan Babban Birnin Tarayya, Muhammed Bello, da takwaransa na jirgin sama, Hadi Sirika, a cewar Punch.

KU KARANTA: Badakalar Abacha: Makudan kudaden da Najeriya ta kwato cikin shekaru 23

Duk masu lalata kayayyakin gwamnati su sani hakan ta'addanci ne, Lai Mohammed
Duk masu lalata kayayyakin gwamnati su sani hakan ta'addanci ne, Lai Mohammed Hoto: dw.com
Asali: UGC

Lai Mohammed ya ce barnar na yin barazana ga rayukan ‘yan kasa kuma suna da illa ga karancin kudaden shigar da gwamnati ke samu yayin da take neman sauyawa, gyara ko kuma sake gina irin kayayyakin more rayuwar da aka lalata.

A nasa bangaren, Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya ce an yi barna mai yawa a kan hanyoyi, gadoji da sauransu.

Ya ce gwamnati za ta kashe sama da N2bn don gyara wasu hanyoyin da aka lalata a kasar.

Ya lissafa kadarorin da aka lalata a karkashin ma'aikatarsa da suka hada da Otedola da Kara Bridges a jihar Lagos, Tamburawa Bridge a jihar Kano, da sauransu.

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce satar abubuwan hanyoyin jirgin kasa na iya haifar da haddura masu saurin kisa.

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya yi kira ga wadanda ke lalata kayayyakin jama'a da su rungumi zaman lafiya.

Shugaban majalisar dattijan wanda Sanata Dauda Yaro ya wakilta, ya nemi ministocin da su gabatar da dokokin da suke so sannan kuma su aika wa majalisar kasa don dubawa.

KU KARANTA: Zan karfafa muku cin naman Alade a madadin na Shanu, Akeredolu ga 'yan jiharsa

A wani labarin, An shiga fargaba a garin Igangan, jihar Oyo, a daren Asabar, 5 ga Yuni, yayin da wasu 'yan bindiga suka tura sama da mutane 45 zuwa kabari.

Sun News ta ruwaito cewa barnar da aka kwashe sa’o’i biyar ana yi a daya daga cikin manyan garuruwan Ibarapaland ta kai ga kone gidaje sama da 60, yayin da sama da motoci 160 kuma suka lalace.

Maharan sun yi kaca-kaca da fadar Ashigangan ta Igangan, Oba Lasisi Adeoye, da kuma wani gidan mai, yayin da suka afka wa al'ummar da misalin karfe 11 na dare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel