Shugaba Buhari Ya Jagoranci Sake Buɗe Makarantar Chibok, Ya Canza Mata Sabon Suna

Shugaba Buhari Ya Jagoranci Sake Buɗe Makarantar Chibok, Ya Canza Mata Sabon Suna

- Shugaban Ƙasa Buhari ya ƙaddamar da sabuwar makarantar Chibok da aka sake ginawa kuma aka canza mata suna

- Shugaban wanda ministan mata, Mrs Pauline Tallen, ta wakilta, yace gwamnatinsa na iya ƙoƙarinta wajen ganin komai ya daidaita a garin Chibok

- Gwamna Zulum, ya godewa shugaba Buhari bisa taimakonsa wajen samar da kuɗin da aka kammala ginin makarantar

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya kaddamar da sake buɗe makarantar sakandiren mata dake garin Chibok, jihar Borno, wanda mayaƙan Boko Haram suka taɓa kaiwa hari, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: NBC Ta Umarci Dukkan Tashoshin Watsa Labarai Su Dakatar da Amfani da Twitter

Sabuwar makarantar an saka mata suna 'makarantar sakandiren gwamnati' saboda yanzun za'a haɗa ɗalibai mata da maza.

A ranar 14 ga watan Afrilu, mayaƙan ƙungiyar ta'addanci Boko Haram suka kai hari makarantar inda suka yi awon gaba da ɗalibai mata 276.

Tun bayan wannan lokacin ne, gwamnatin tsohon shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ta ofishin minitar kuɗinsa, Dr Ngozi Okonjo Iwella, ta ɗora tubalin sake gina makarantar.

Shugaba Buhari Ya Jagoranci Sake Buɗe Makarantar Chibok, Ya Canza Mata Sabon Suna
Shugaba Buhari Ya Jagoranci Sake Buɗe Makarantar Chibok, Ya Canza Mata Sabon Suna Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Bayan zuwan shugaba Buhari a 2015 da kuma sabon gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, suka ɗora daga inda tsohuwar gwamnati ta tsaya.

Duk da cewa wasu daga cikin ɗaliban da yan Boko Haram suka sace sun gudo, har yanzun akwai kusan guda 112 dake hannun su, ana raɗe-radin ma sun aurar da su ga junan su.

KARANTA ANAN: Muhimman Hanyoyi 6 da Hana Amfani da Twitter Zai Shafi Yan Najeriya da Kasuwancinsu

Buhari, wanda ministan harkokin mata, Mrs Pauline Tallen, ta wakilta, tace ta zo jihar ne don ta isar da saƙon shugaba Buhari ga mutanen Borno, musamman mazauna garin Chibok.

Ministan ta yi godiya ga gwamnatin Borno bisa jajircewarta wajen ganin an gama ginin makarantar.

Tace: "Muna ƙara jajantawa mazauna garin Chibok, mun san halin da kuke ciki, amma ina tabbatar muku muna aiki ba dare ba rana wajen ganin komai ya dai-daita a Chibok da dukkan yankunan da matsalar tsaro ta shafa."

"Ina mai kara roƙon shugabannin Chibok da su cigaba da taimakawa gwamnatin jihar Borno ƙarakashin jagorancin gwamna Zulum, wanda a shirye yake ya baiwa ilimin ƴaƴa mata duk abinda yake buƙata."

A jawabinsa, gwamnan Borno, Babagana Zulum, yayi godiya ga shugaba Buhari da ya taimaka wa gwamnatin jihar ta samu kuɗin da ake buƙata har aka kammala ginin.

Gwamnan ya kuma yi addu'a, Allah ya kuɓutar da sauran ɗaliban da suke hannun yan ta'adda.

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Kare Kansa, Ya Bayyana Dalilin Gwamnatinsa Na Dakatar da Twitter a Najeriya

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yace gwamnatinsa ba zata cigaba da zura ido a kan abinda twitter ke yi a Najeriya ba, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Yace daman can kamfanin na wuce gona da iri wajen yaɗa kalaman addini, wariya, kiyayya da dai sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel