Zan karfafa muku cin naman Alade a madadin na Shanu, Akeredolu ga 'yan jiharsa

Zan karfafa muku cin naman Alade a madadin na Shanu, Akeredolu ga 'yan jiharsa

- Gwamnan jihar Ondo ya bayyana aniyarsa ta karfafa maciya naman alade a duk fadin jihar

- Ya ce gwamnatinsa a shirye take don maye gurbin naman shanu da naman alade a fadin jihar

- A cewarsa, jihar na asarar kudaden da ya kamata a jihar za a kashesu ga wasu jihohin daban

Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya ce gwamnatinsa za ta karfafa cin naman alade a madadin naman shanu don tattala miliyoyin nairorin da jihar ke asara ga sauran jihohin da ke samar da naman shanu da sauran nau'ikan nama, Daily Trust ta ruwaito.

Akeredolu ya fadi haka ne a ranar Litinin yayin kaddamar da wani babban mayankar alade ta Dutchman Piggery da kayan tallafi a Ilutoro da ke karamar hukumar Akure ta Arewa a jihar a matsayin wani bangare na ayyukan cikarsa kwanaki 100 a ofis.

KU KURANTA: Rahoto: ISWAP ta tabbatar da mutuwar Shekau, ta ce Shekau dan rashawa ne

Ku ci naman alade maimakon na shanu: Gwamnan Ondo ya yi martani kan rikicin makiyaya
Ku ci naman alade maimakon na shanu: Gwamnan Ondo ya yi martani kan rikicin makiyaya Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A cewar gwamnan, kudin da ake kashewa ga wasu jihohin da ke samar da shanu da sauran nau'ikan nama zasu kasance a jihar don kara tattalin arzikin jihar.

Ya kuma ce baya ga ayyukan ta da zai samar wa matasa, za a karfafawa masu cin naman alade, naman alade kuma zai zama madadin naman shanu a jihar.

"Bugu da kari, za a kuma karfafa yankunan mu na karkara don ci gaba.

“Abin mamaki ne cewa miliyoyin Nairori suna barin wannan Jiha duk mako saboda cin naman shanu.

A baya an samu tangarda tsakanin gwamnatin jihar ta Ondo da makiyaya dake zaune a yankunan jihar, lamarin da ya kai ga ba da umarnin fatattakar makiyaya a fadin Ondo, Vanguard ta ruwaito.

KU KARANTA: Tuna baya: Hotunan marigayi TB Joshua na aikin alheri sun bar mutane cikin jimami

A wani labarin, Kungiyar manoma Albasa da kasuwancinta a Najeriya (OPMAN) ta ce za ta katse samar da kayayyaki ga dukkan yankunan kudancin Najeriya daga ranar Litinin matukar gwamnatoci ba su amsa bukatun kungiyar ba.

Daily Trust ta tattaro cewa daya daga cikin bukatun OPMAN shi ne cewa membobin kungiyar da suka yi asara sakamakon rikicin kabilanci da addini a Kudancin dole ne a biya su yadda ya kamata.

Sauran sun hada da maido da doka da oda a wadannan yankuna tare da yin cikakken bincike don gano musabbabin wadannan hare-hare kan mambobinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.