Tuna baya: Hotunan marigayi TB Joshua na aikin alheri sun bar mutane cikin jimami

Tuna baya: Hotunan marigayi TB Joshua na aikin alheri sun bar mutane cikin jimami

- Duniya ta shiga jimamin rashin da ta yi na babban malamin addinin kirista, TB Joshua na Najeriya

- An bayyana wasu hotuna dake nuna babban malamin yana aikata ayyukan alheri ga mutanensa

- Hakazalika 'yan Najeriya da dama sun yi sharhi kan hotunan, in da suka bayyana jimaminsu tare da yi masa addu'a

Duniya ta fada cikin jimami yayin da shahararren malamin addinin kirista nan kuma mai kula da cocin Synagogue Church of all Nations (SCOAN), TB Joshua, ya mutu da sanyin safiyar Lahadi, 6 ga Yuni.

Jinjina da yabo ga malamin na SCOAN ya mamaye dandamali na dandalin sada zumunta yayin da mutane ke magana game da yawan ayyukan sa na alheri.

A ranar Lahadin nan, wani a shafin Facebook kuma mabiyin marigayin, Prince Toyin Akingbade, ya watsa hotunan malamin wanda ya kara tabbatar da abin da mutane ke fadi game da shi.

KU KARANTA: Rahoto: ISWAP ta tabbatar da mutuwar Shekau, ta ce Shekau dan rashawa ne

Tuna baya: Hotunan marigayi TB Joshua na aikin alheri ya bar 'yan Najeriya baki bude
Tuna baya: Hotunan marigayi TB Joshua na aikin alheri ya bar 'yan Najeriya baki bude Hoto: Prince Toyin Akingbade
Asali: Facebook

A cikin daya daga cikin hotunan, malamin ya dauki buhunan abinci uku a kansa, yana gumi a cikin taguwarsa. Wani hoton kuma ya nuna yana ba da kayan abinci mai yawa ga mutanen da suke bukata.

A cikin wani hoto, an ganshi yana tsaftace cocin yayin da ya fara aikin share kujerun da suka yi datti da kura.

Ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, wallafawar ta facebook ta sami sama da dangwale 800 tare da dubun tsokaci. Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin su a kasa:

Olayiayo Afun ya ce:

"Duniya za ta yi kewarsa saboda duk abin da kake ambata a nan na abin da ke iya karewa a duniya ne, addu'ata a gare shi ita ce aljanna ta zama makomarsa."

Adeyemi Thomas Idowu ya ce:

"Duk wani fasto dan Najeriya da zai shiga aljanna, T B Joshua zai zama na daya! RIP bawan Allah!"

Adu Dapo ya ce:

"Babban rashi ne ga wannan duniya mai lalacewa, Za mu ci gaba da tunawa da shi saboda tasirin sa da kyawawan abubuwan da ya bari."

Richy Kool ya ce:

"Babu wani kamarsa a duk duniya .. mutanen duniya tabbas zasuyi kewarka tuni na yi kewarka abin kaunata."

KU KARANTA: Dillalan albasa za su katse kai kaya zuwa Kudancin Najeriya daga ranar Litinin

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya jajanta wa iyalai da mabiya fastor Temitope Balogun wanda aka fi sani da TB Joshua kan mutuwarsa.

Shugaban ya ce za a yi kewar fitataccen malamin na Kirista musamman mabiyansa da kuma duniya baki daya kan gudunmuwarsa ga mutane ta hanyar ayyukansa na taimako.

Ya kuma jajantawa gwamnati da mutanen jihar Ondo kan rashin da suka yi na Fasto TB Joshua.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.