Shugaba Buhari Ya Kare Kansa, Ya Bayyana Dalilin Gwamnatinsa Na Dakatar da Twitter a Najeriya

Shugaba Buhari Ya Kare Kansa, Ya Bayyana Dalilin Gwamnatinsa Na Dakatar da Twitter a Najeriya

- Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yace gwamnatinsa ba zata cigaba da zura ido a kan abinda twitter ke yi a Najeriya ba

- Yace daman can kamfanin na wuce gona da iri wajen yaɗa kalaman addini, wariya, kiyayya da dai sauransu

- Shugaban ya faɗi haka ne a wani jawabin da kakakinsa, Malam Garba Shehu, ya fitar yau Asabar

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya kare matakin gwamnatinsa na dakatar da Twitter a Najeriya, yace daman shafin yana taka rawa wajen rura wutar rikici a ƙasa, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: NLC Ta Aike Wa Buhari Wasiƙa, Tayi Barazanar Sake Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa a Kan El-Rufa’i

A wani jawabi da kakakin shugaban, Malam Garba Shehu, ya fitar Ranar Asabar, yace gwamnatin Buhari ba zata bar shafin sada zumunta ya raba Najeriya ba.

Ya kuma masanta zargin cewa gwamnati ta ɗauki wannan matakin ne saboda twitter ya goge rubutun shugaba Buhari.

Shugaba Buhari Ya Kare Kansa, Ya Bayyana Dalilin Gwamnatinsa Na Dakatar da Twitter a Najeriya
Shugaba Buhari Ya Kare Kansa, Ya Bayyana Dalilin Gwamnatinsa Na Dakatar da Twitter a Najeriya Hoto: @BashirAhmad
Asali: Instagram

A rahoton BBC Buhari yace ya zama wajibi dandalin sada zumuntar ya girbi abinda ya shuka.

Shugaba Buhari yace:

"Dakatar da twitter na wucin gadi da mukayi ba wai martani ne ga goge rubutun shugaba Buhari da kamfanin yayi bane, daman kamfanin yana yaɗa ƙarya, kalaman addini, wariyar launin fata, kiyayya da sauransu waɗanda ke taka rawa wajen haddasa rikici tsakanin yan Najeriya."

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: MTN, Airtel, Glo Sun Rufe Damar Shiga Twittter a Najeriya

Shugaban ya ƙara da cewa kalaman da yayi na gargaɗi ga masu tada wutar rikici a yankin kudu maso gabashin ƙasar ba barazana bace, kuma abin haushe ne ace shafin ya cire su.

"Daman kamfanin ya daɗe yana kawo mana matsala a Najeriya, twitter na wuce gona da iri," inji Buhari.

A wani labarin kuma Gwamna Ya Dakatar da Biyan Mafi Ƙarancin Albashi, Ya Zabtare Albashin Ma’aikatan Jiharsa

Gwamnatin jihar Ekiti ƙarƙashin jagorancin Kayode Fayemi, ta dakatar da biyan mafi ƙarancin albashi ga wani rukunin ma'aikatan jihar.

Wanna na ƙunshe ne a wata yarjejeniya da aka cimma wa tsakanin gwamnatin da ƙungiyoyin ƙwadugo na jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel