Rundunar Yan Sanda Ta Ragargaji Wasu Yan Fashi 5 a Jihar Benuwai
- Wasu Yan fashi ɗauke da makami sun gamu da ajalinsu yayin da Suka shiga gida-gida domin yin sata a Ugba
- Rundunar yan sanda ta yankin ce ta samu nasarar hallaka biyar daga cikin su bayan fafatawar da duka yi
- Rahotanni sun tabbatar da faruwar lamarin, kuma wasu daga cikin jami'an yan sanda sun samu raunuka yayin fafatawar
Jami'an yan sanda sun kashe wasu da ake zargin yan fashi da makami ne a Ugba, hedkwatar karamar hukumar Logo, jihar Benuwai, kamar yadda the nation ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Muhimman Abubuwa 7 da Ya Kamata Ku Sani Game da Marigayi T. B Joshua
Yan fashin da aka kashe ɗin, sun addabi mutanen yankin Ugba da satar mutane, Sata, fashi da makami da sauransu tun watanni 5 da suka wuce.
Wani mazaunin garin Ugba, ya bayyana cewa yan fashin sun yi wa DPO na yankin barazanar kisa ko kuma ya nemi a canza masa wurin aiki.
Legit.ng hausa ta gano cewa yan fashin sun gamu da ajalinsu ne yayin da suka je Operation, suka shiga gida-gida suna ƙwace wa mazauna garin dukiyoyin su ranar Jumu'a da daddare.
Jami'an yan sanda sun kai ɗauki bayan ɗaya daga cikin mazauna garin ya sanar da su ta wayar salula.
KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Kare Kansa, Ya Bayyana Dalilin Gwamnatinsa Na Dakatar da Twitter a Najeriya
Bayan musayar wuta tsakanin jami'an yan sanda da ɓarayin, an kashe 5 daga cikin su yayin da wasu yan sanda suka samu raunuka.
Wani ɗan sanda dake yankin wanda ya nemi a sakaya sunan shi ya tabbatar da faruwar lamarin, amma yace a tuntuɓi hedkwatar yan sandan jihar Benuwai domin ƙarin bayani.
Yace: "Eh, yan sanda sun kashe mutum biyar daga cikinsu, amma ku tuntuɓi hedkwatar jiha."
A wani labarin kuma NLC Ta Aike Wa Buhari Wasiƙa, Tayi Barazanar Sake Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa a Kan El-Rufa’i
Ƙungiyar kwadugo ta ƙasa, NLC, ta turawa shugaba Buhari wasiƙa cewa zata shiga yajin aiki na ƙasa a kan gwamnatin Kaduna, kamar yadda daily Nigerian ta ruwaito.
NLC tace gwamnatin Kaduna tayi fatali da MoU da aka cimmawa a taron sulhu da FG ta shirya wa ɓangarorin biyu.
Asali: Legit.ng