2023: Nan Gaba Ƙaɗan Wasu Gwamnonin PDP Zasu Sauya Sheƙa Zuwa APC, Ganduje

2023: Nan Gaba Ƙaɗan Wasu Gwamnonin PDP Zasu Sauya Sheƙa Zuwa APC, Ganduje

- Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa nan gaba kaɗan APC zata yi sabbin gwamnoni daga jam'iyyar PDP

- Gwamna Ganduje yace tuni jam'iyya mai mulki ta fara shirye-shiryen tarbar gwamnonin

- Ganduje ya faɗi haka ne yayin da kwamitin rijistar zama mamban APC na ƙasa ya kai masa ziyara a Abuja

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa jam'iyya mai mulki ta fara shirye-shiryen karɓar wasu gwamnonin PDP a dai-dai lokacin da zaɓen 2023 ke ƙaratowa, kamar yadda daily Nigerian ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Kare Kansa, Ya Bayyana Dalilin Gwamnatinsa Na Dakatar da Twitter a Najeriya

Idan zaku iya tunawa a baya-bayan nan Legit.ng hausa ta kawo muku rahoton sauya sheƙar gwamnan Cross Rivers, Ben Ayade, daga PDP zuwa APC.

Yayin da a kwanan nan ake ta raɗe-raɗin gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ka iya komawa APC a ko wane lokaci, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

2023: Nan Gaba Ƙaɗan Wasu Gwamnonin PDP Zasu Sauya Sheƙa Zuwa APC, Ganduje
2023: Nan Gaba Ƙaɗan Wasu Gwamnonin PDP Zasu Sauya Sheƙa Zuwa APC, Ganduje Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Ganduje ya faɗi haka ne yayin da kwamitin rijista na APC ya kai masa ziyara a gidan gwamnatin Kano dake Abuja, wanda Farouk Adamu Aliyu, yake jagoranta.

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Banka Wuta a Gidan Kwamishinan Jihar Imo

Gwamnan yace: "Ina mai sanar daku cewa akwai alamun wasu gwamnoni zasu dawo jam'iyyar mu ta APC daga wasu jam'iyyu. Jam'iyyar mu na ƙara ƙarfi a kullum."

Ganduje ya musanta zargin cewa an yiwa wasu mambobin APC maguɗi yayin gudanar da rijista da kuma sabunta rijistar a jihar Kano, inda aka jiyo shi yana cewa:

"Babu wanda aka yiwa maguɗi a lokacin, amma duk wanda ke ganin an mishi maguɗi kofar mu a buɗe take, a shirye muke mu yiwa kowa rijista, ba ruwanmu da ra'ayinsa game da APC."

A wani labarin kuma Muhimman Abubuwa 7 da Ya Kamata Ku Sani Game da Marigayi T. B Joshua

Malamin majami'ar dukkan ƙasashe, T. B Joshua ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 57 a duniya, kamar yadda the nation ta ruwaito.

An haifi Joshua ne a ranar 12 ga watan Yuni 1963, ya rasu gab da zagayowar ranar haihuwarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel