Bayan shekaru 5 na aiki tukuru, beran da ya ci lambar yabon zinare ya yi ritaya

Bayan shekaru 5 na aiki tukuru, beran da ya ci lambar yabon zinare ya yi ritaya

- Rahotanni sun bayyana yadda wani bera mai ban al'ajabi ya yi aiki tukuru wajen ceto rayuka

- An ba beran lambar yabo na zinare bayan share shekaru yana aiki ba kakkautawa wa al'umma

- An ruwaito cewa, beran ya yi ritaya bayan nuna gajiya da tsufa duk da yana cikin koshin lafiya

Wani gwarzon bera da aka yi bikin saboda iya binciken nakiyoyin da aka binne ya kusa shiga wani ritayar da ta cancanta.

Beran mai suna Magawa haifaffen Tanzania yana da tarihin aiki na tsawon shekaru biyar wanda ya kai ga ceton rayukan maza da mata, da yara da manya wadanda barkewar abubuwan fashewa da ragowar yaki ya shafa.

Wata kungiyar kasar Belgium mai suna Apopo ce ta horas da beran mai shekara bakwai, wanda dan asalin kasar Tanzaniya ne kuma tana horas da dabbobi domin gano abubuwan fashewa da aka binne a karkashin kasa da kuma masu dauke da cutar tarin fuka a shekarun 1990.

KU KARANTA: An cafke matashin da ya dabawa matar dan uwansa mai ciki wuka a jihar Kano

Bayan shekaru 5 na aiki tukuru, beran da ya ci lambar zinare ya yi ritaya daga aiki
Bayan shekaru 5 na aiki tukuru, beran da ya ci lambar zinare ya yi ritaya daga aiki Hoto: Sahel Hausa
Asali: Facebook

Ana bai wa dabbobin lambar yabo bayan shekara daya idan aka gama horas da su, rahoton BBC.

A cewar APOPO, kungiyar da ta horar da Magawa, wanda yanzu haka ke a kasar Kambodiya, shahararren beran na Afirka ya gaji sannu a hankali amma yana cikin koshin lafiya.

APOPO ta ce a ranar Alhamis, 3 ga Yuni:

"Duk da cewa har yanzu yana cikin koshin lafiya, ya kai shekarun ritaya kuma a fili ya fara gajiya. Lokaci ya yi."

An haifi jarumin beran ne a kasar Tanzania a watan Nuwamba na shekarar 2014. Ya girma ne a Cibiyar Horaswa da Bincike ta APOPO a Tanzania, inda ya koyi yadda ake sansana da abubuwan fashewa.

Daga nan Magawa ya koma Siem Reap a cikin Kambodiya a shekarar 2016, inda ya fara aikinsa.

A lokacin da yake aiki, Magawa ya gano nakiya 71 da abubuwa 38 na bama-bamai da ba su fashe ba, wanda hakan ya sa ya zama gwarzon bera na cibiyar APOPO..

A cikin shekaru biyar da suka gabata, ya taimaka wajen share sama da murabba'in mita 225,000, yana ba wa al'ummomin yankin damar zama, aiki, wasa da neman ilimi ba tare da tsoron rasa rai ko wata gabar jiki ba.

A watan Satumba na 2020, Magawa ya sami lambar yabo ta zinare saboda jaruntakarsa, sadaukar da rai da himma kan aiki.

An gabatar da Magawa bisa ka'ida tare da karamar lambar yabon zinare ta PDSA, kwatankwacin dabbar George Cross.

Cibiyar Kula da Ma'adinai ta Kambodiya ta ba da rahoton cewa Kambodiya na iya zama a kan sama da nakiyoyi miliyan shida da kuma wasu abubuwa da ba a fashe ba.

KU KARANTA: Dakatar da Twitter: Gwamnati ta ba da alamar yaushe za a dawo yin Twitter

A wani labarin, Shahararren mawaki, Naira Marley ya bayyana cewa zai yi zaman jira don rera sabuwar wakar taken kasa bayan yanke shawarar sauya sunan Najeriya zuwa Hadaddiyyar Jamhuriyar Afirka (UAR).

A cewar rahotanni, Adeleye Jokotoye, kwararre kan haraji, ya gabatar da shawarar ga kwamitin a taron sauraron kararrakin yankin Kudu maso Yamma da ke Legas a ranar Laraba, 2 ga Yuni, 2021, jaridar Pulse ta ruwaito.

Yayin da yake gabatar da wannan shawara, ya ce sunan Najeriya turawan mulkin mallaka ne suka tilastawa kasar kuma ya kamata a canza shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel