An cafke matashin da ya dabawa matar dan uwansa mai ciki wuka a jihar Kano

An cafke matashin da ya dabawa matar dan uwansa mai ciki wuka a jihar Kano

- Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta samu nasarar kame wani yaron da ya kashe matar yayansa

- Rahotanni sun bayyana cewa, matar na dauke da ciki, kuma dan cikin ya mutu bayan an je asibiti

- Hakazalika an kame wasu mutane da laifin kashe wata mata mai suna Humaira duk dai a jihar Kano

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta tabbatar da cafke wani yaro dan shekara 15 da ya dabawa matar dan uwansa 'yar shekara 25 wuka.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da DSP Abdullah Aaron, kakakin ‘yan sanda a jihar ya fitar., Daily Trust ta ruwaito.

DSP Haruna ya bayyana cewa: “Misalin karfe 11 na dare, an samu wani korafi cewa wanda ake zargin ya dabawa Misis Habiba Isah wacce ke dauke da ciki wata takwas wuka.

KU KARANTA: Dakatar da Twitter: Gwamnati ta ba da alamar yaushe za a dawo yin Twitter

'Yan sanda sun cafke wani matashi da ya dabawa matar dan uwansa wuka a jihar Kano
'Yan sanda sun cafke wani matashi da ya dabawa matar dan uwansa wuka a jihar Kano Hoto: pulse.ng
Asali: UGC

“Bayan samun rahoton, 'yan sanda sun ziyarci inda lamarin ya faru kuma an kai matar zuwa Asibitin Koyarwa na Aminu Kano inda aka kwantar da ita sannan daga baya aka tabbatar da cewa jaririn da ke ciki ya mutu.”

Haruna ya ce karamin yaron ya ziyarci gidan dan uwan nasa, inda ya bukaci ganin matar dan uwan nasa.

Ya ce matar “ta tsorata kuma ta kira mijinta, amma yaron ya buge wayar daga hannunta da tabarya. Sannan ya caka mata wuka a ciki da sauran sassan jikinta.”

A wani rahoton jaridar Pulse, rundunar ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da kisan Humaira Abubakar, a Unguwar Danbare da ke cikin jihar ta Kano.

Kwamishinan ‘yan sanda, Mista Sama’ila Dikko, ya ce ya ba da umarnin a tura karar zuwa sashen kisan kai na sashen binciken manyan laifuka na rundunar (CID) don gudanar da bincike.

Ya kara da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu idan sun kammala bincike.

KU KARANTA: Ku kirkiri taku kafar: APC ta kalubalanci matasan Najeriya bayan hana Twitter

A wani labarin, Wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun kai hari bankunan kasuwanci biyu da ofisoshin ‘yan sanda da yammacin Laraba a garin Apomu da Ikire da ke jihar Osun.

A yayin harin, an samu labarin cewa ‘yan fashin sun harbe mutane da yawa, duk da cewa rundunar 'yan sanda ta jihar ta ce ba ta samu adadin wadanda suka rasa rayukansu ba.

An ce barayin sun shiga Apomu da Ikire ta cikin garin Ikoyi kuma sun kasa kansu zuwa gungu daban-daban kafin su fara kai hari kan ofisoshin ‘yan sanda da bankunan da abin ya shafa, jaridar Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.