An dakile harin 'yan ta'adda a hedkwatar 'yan sanda ta Imo, an hallaka tsageru 5

An dakile harin 'yan ta'adda a hedkwatar 'yan sanda ta Imo, an hallaka tsageru 5

- Rundunar 'yan sanda a jihar Imo ta bayyana cewa ta hallaka wasu tsagerun mahara biyar

- Rahotanni sun ce, 'yan ta'addan sun kai hari ne hedkwatar 'yan sanda ta jihar Imo a karo na biyar

- An kwato bindogogi tare da motar da suka kai harin da ita, inda ake ci gaba da bincike kan lamarin

Rundunar ‘yan sanda a jihar Imo ta ce ta dakile wani hari da wasu 'yan ta'adda suka kaiwa hedikwatar ‘yan sanda a jihar a ranar Lahadi, inda suka kashe biyar daga cikin maharan.

Wannan shi ne karo na biyu da ‘yan bindiga suka far wa hedikwatar 'yan sanda ta Imo da ke Owerri tun lokacin da aka fara barnata hukumomin tsaro a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda a jihar, SP Bala Elkana, a cikin wata sanarwa ya ce maharan sun mamaye hedkwatar ne a safiyar ranar Lahadi amma suka fuskantar turjiya daga jami'an 'yan sanda, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Ku kirkiri taku kafar: APC ta kalubalanci matasan Najeriya bayan hana Twitter

An dakile harin 'yan ta'adda a hedkwatar 'yan sanda ta Imo, an hallaka tsageru 5
An dakile harin 'yan ta'adda a hedkwatar 'yan sanda ta Imo, an hallaka tsageru 5 Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Vanguard ta ruwaito PPRO din ya cewa: “Wasu 'yan ta'adda da ke yin shigar 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi yunkurin kai hari a Hedikwatar 'yan sanda da safiyar yau amma an dakile su.

“Sun yi kokarin shiga Hedikwatar 'yan sanda ta hanyar Layout Works da ke kusa da makarantar Nazire da Firamare ta Avan amma an hanasu da karfi.

“Sun zo ne a cikin farar motar Hummer. Biyar daga cikin maharan sun mutu yayin musayar wuta kuma wasu sun ji rauni.

“An kwace motar Hummer din. An kuma kwato bindigogin Ak47 guda hudu,” sanarwar ta kara da cewa.

KU KARANTA: Bayan shekaru 5 na aiki tukuru, beran da ya ci lambar yabon zinare ya yi ritaya

A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta tabbatar da cafke wani yaro dan shekara 15 da ya dabawa matar dan uwansa 'yar shekara 25 wuka.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da DSP Abdullah Aaron, kakakin ‘yan sanda a jihar ya fitar., Daily Trust ta ruwaito.

DSP Haruna ya bayyana cewa: “Misalin karfe 11 na dare, an samu wani korafi cewa wanda ake zargin ya dabawa Misis Habiba Isah wacce ke dauke da ciki wata takwas wuka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel