Bukola Saraki Da Atiku Sun Yi Martani Kan Dakatar Da Kafar Sada Zumuta Ta Twitter

Bukola Saraki Da Atiku Sun Yi Martani Kan Dakatar Da Kafar Sada Zumuta Ta Twitter

- 'Yan Najeriya sun fara bayyana martaninsu biyo bayan dakatar da kamfanin Twitter a Najeriya

- Tsohon shugaban majalisar dattawa shi ma ya tofa nashi albarkacin baki ta shafin na Twitter

- Hakazalika tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar shi ma ya bayyana nasa ra'ayin

Kafafen sada zumunta sun cika da cece-kuce biyo bayan umarnin gwamnatin Buhari na dakatar da ayyukan Twitter a fadin kasar saboda goge rubutun shugaban kasa da Twitter din ta yi.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar da kuma tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya Abubakar Bukola Saraki, sun tofa albarkacin bakinsu kan umarnin na gwamnatin Buhari.

A wasu rubutun da Legit.ng Hausa ta gano na jiga-jigan 'yan siyasan, ta gano inda suke martani kan batun.

KU KARANTA: Dakatar Da Twitter: Shehu Sani Ya Bayyana Hanya Mafi Sauki Don Hawa Twitter

Bukola Saraki Da Atiku Sun Yi Martani Kan Dakatar Da Shafin Twitter
Bukola Saraki Da Atiku Sun Yi Martani Kan Dakatar Da Shafin Twitter Hoto: obyoriji.com
Asali: UGC

Bukola Saraki ya rubuta:

"A'a yallabai! Wannan bai kamata ya zama martani daga shugaban kasar da ke da dimbin matasa wadanda #Twitter ta zama jigon rayuwarsu na yau da kullum kuma tushen samun kudin shiga da rayuwarsu ba.
"Dole ne a sake duba lamarin."

Atiku Abubakar kuma yace:

"Da fatan, wannan ba shine rubutu na a Twitter na karshe ba. #murmushi"

Umarnin dai ya tabbata, domin tuni kamfanonin sadarwa suka karbi umarnin katange 'yan Najeriya daga samun damar isa ga shafin na Twitter, The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA: Ya kamata Twitter ta bar Najeriya: Adamu Garba ya caccaki Twitter saboda Buhari

A wani labarin, A yau ne aka tashi da labarin da ya jawo cece-kuce tsakanin 'yan Najeriya, inda kowa yake tofa albarkacin bakinsa a matsayin dan kasa mai kishi.

An bada shawarin sauyawa Najeriya suna zuwa Hadaddiyar Janhuriyar Afrika wacce turance take nufin 'United African Republic' a takaice kuwa, UAR.

Wasu shahararren 'yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu game da shawarin sauyin, wanda Legit.ng Hausa ta tattarowa mabiyanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.