NCC Ta Ba Kamfanonin Sadarwa Umarnin Hana ’Yan Najeriya Damar Hawa Twitter

NCC Ta Ba Kamfanonin Sadarwa Umarnin Hana ’Yan Najeriya Damar Hawa Twitter

- Biyo bayan dakatar da kamfanin Twitter a Najeriya, NCC ta bada umarni ga kamfanonin sadarwa su aiwatar da umarnin

- Kamfanonin sun bayyana goyon bayansu ga gwamnatin Najeriya wajen kawo wa 'yan kasa ci gaba mai amfani

- Sai dai, kamfanin na Twitter ya bayyana rashin jin dadinsa, tare da cewa babban abun damuwa ne dakatarwar

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, kamfanonin sadarwa a Najeriya sun ce sun samu umarni daga Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) don aiwatar da dakatar da ayyukan karamin shafin yanar gizo na Twitter.

Kamfanonin da ke aiki a karkashin kungiyar masu lasisi na kamfanonin sadarwar na Najeriya (ALTON), sun ce sun gudanar da aikin tantance bukatar bisa ga kyakkyawan tsarin duniya.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Hukumar Jarrabawar NECO Ta Nada Sabon Shugaban Riko

NCC ta ba kamfanonin sadarwa umarnin hana 'yan Najeriya damar hawa Twitter
NCC ta ba kamfanonin sadarwa umarnin hana 'yan Najeriya damar hawa Twitter Hoto: angeladaviesblog.com.ng
Asali: UGC

Shugabanta, Gbenga Adebayo, a cikin wata sanarwa, ya ce:

“Mu, kungiyar masu lasisi na kamfanonin sadarwar na Najeriya (ALTON), muna son tabbatarwa cewa mambobinmu sun karbi umarni daga Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), mai kula da masana'antun da su dakatar samun damar isa ga Twitter.
“ALTON ta gudanar da cikakken bincike kan bukatar daidai da ka’idojin da duniya ta yarda da su.
“Dangane da tanade-tanaden da suka shafi maslahar kasa a cikin Dokar Sadarwar Najeriya, 2003, kuma a tsakanin ka’idojin lasisi da masana’antar ke aiki a karkashinsa; membobinmu sun yi aiki daidai da umarnin NCC, mai kula da masana'antun.

Hakazalika kungiyar ta jaddada goyon bayanta ga gwamnatin Najeriya da matakan da take dauka na kawo wa 'yan kasar ci gaba mai amfani.

Sai dai, The Cable ta ruwaito cewa, biyo bayan umarnin dakatar da ayyukan na Twitter a Najeriya, kamfanin ya bayyana matukar damuwarsa da yanayin, in da yake cewa:

“Sanarwar da Gwamnatin Najeriya ta bayar cewa sun dakatar da ayyukan Twitter a Najeriya babban abun damuwa ne.
"Muna bincike kuma za mu samar da abubuwan sabuntawa lokacin da muka samu."

KU KARANTA: Ra'ayoyin 'Yan Kasa Kan Kudurin Sauyawa Najeriya Suna 'United African Republic'

A wani labarin, Adamu Garba, wani tsohon dan takarar shugaban kasa a Najeriya ya caccaki kamfanin Twitter bisa goge jawabin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kan masu kokarin kifar da gwamnatinsa.

A makon nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jawabi ta shafin Twitter cewa, duk masu kokarin kitsa kifar da gwamnatinsa su shirya za su shiga firgici, kuma zai musu magana da yaren da suka fi fahimta, amma kamfanin ya goge rubutun.

A wani rubuta da wakilin Legit.ng Hausa ya gani daga shafin Adamu Garba, ya gano inda matashin kuma tsohon dan takarar shugaban kasa ke caccakar shawarar da Twitter ta yanke na goge rubutun, yana mai kira ga tattarawar Twitter ta bar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel