Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 5 Akan Hanyar Zaria Zuwa Kaduna da Wasu Ƙauyuka

Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 5 Akan Hanyar Zaria Zuwa Kaduna da Wasu Ƙauyuka

- Yan bindiga sun kaiwa matafiya hari a kan hnyar Zaria zuwa Kaduna, inda suka hallaka mutum uku tare da jikkata wasu

- Hakanan kuma wasu mutane ɗauke da makamai sun kai hari ƙauyen Kabai inda suka kashe mutum biyu, suka jikkata wasu biyu

- Kwamishinan tsaro da al'amuran cikin gida, Samuel Aruwan, shine ya bayyana haka, yace gwamna ya jajantawa waɗanda abun ya shafa

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da kashe wasu matafiya uku da kuma wasu mutum biyu da yan bindiga suka yi a cikin jihar, kamar yadda daily Nigerian ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: MTN, Airtel, Glo Sun Rufe Damar Shiga Twittter a Najeriya

Kwamishinan tsaro da al'amuran cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, yace jami'an tsaro sun kaiwa gwamnati rahoton kashe mutum uku da jikkata wasu da dama a yankin Lambar Zango kan hanyar Zaria-Kaduna, ƙaramar hukumar Igabi.

"Mutanen sun rasa rayuwarsu ne lokacin da yan bindiga suka kai musu hari," inji kwamishinan.

Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 5 Akan Hanyar Zaria Zuwa Kaduna da Wasu Ƙauyuka
Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 5 Akan Hanyar Zaria Zuwa Kaduna da Wasu Ƙauyuka Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Mr. Aruwan ya ƙara da cewa jami'an tsaro sun sake kawo wani rahoton na daban, cewa wasu mutum biyu sun rasa tayuwarsu tare da wasu biyun da suka jikkata a yankin Kabai, ƙaramar hukumar Chukun.

Yace maharan sun ƙona ginin wata coci da kuma wani gida guda ɗaya lokacin da suka kai harin, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

KARANTA ANAN: NLC Ta Aike Wa Buhari Wasiƙa, Tayi Barazanar Sake Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa a Kan El-Rufa’i

Yace: "Waɗanda aka kashe a harin sune Zakka Kure da Dare Daudu. Sannan akwai matan malamin cocin da suka ji raunuka kuma a yanzun haka suna amsar kulawa a asibiti mai zaman kanshi, matan sune; Maryamu Daniel da Naomi Daniel."

Gwamnan jihar, Malam Nasiru El-Rufa'i yayi ta'aziyya ga iyalan waɗanda aka kashe, sannan yayi addu'ar samun lafiya ga waɗanda ke kwance a asibiti.

Hakanan kuma gwamnan ya umarci hukumar bada agajin gaggawa NEMA, ta gaggauta zuwa ta duba ɓarnar da maharan sukai a coci da sauran gine-gine a ƙauyen Kabai.

A wani labarin kuma Gwamna Ya Dakatar da Biyan Mafi Ƙarancin Albashi, Ya Zabtare Albashin Ma’aikatan Jiharsa

Gwamnatin jihar Ekiti ƙarƙashin jagorancin Kayode Fayemi, ta dakatar da biyan mafi ƙarancin albashi ga wani rukunin ma'aikatan jihar, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Wannan na ƙunshe ne a wata yarjejeniya da aka cimma wa tsakanin gwamnatin da ƙungiyoyin ƙwadugo na jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262