NLC Ta Aike Wa Buhari Wasiƙa, Tayi Barazanar Sake Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa a Kan El-Rufa’i

NLC Ta Aike Wa Buhari Wasiƙa, Tayi Barazanar Sake Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa a Kan El-Rufa’i

- Ƙungiyar kwadugo ta ƙasa, NLC, ta turawa shugaba Buhari wasiƙa cewa zata shiga yajin aiki na ƙasa a kan gwamnatin Kaduna

- NLC tace gwamnatin Kaduna tayi fatali da MoU da aka cimmawa a taron sulhu da FG ta shirya wa ɓangarorin biyu

- Ƙungiyar tace matuƙar gwamnatin ta cigaba da aikata haka to zasu koma yajin aiki kuma wannan lokacin a ƙasa baki ɗaya

Ƙungiyar ƙwadugo ta ƙasa, NLC, ta aikewa Buhari wasiƙa akan rashin aiwatar da yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da ƙungiyar ta sanyawa hannu tare da gwamnatin Kaduna, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Gwamna Ya Dakatar da Biyan Mafi Ƙarancin Albashi, Ya Zabtare Albashin Ma’aikatan Jiharsa

Ƙungiyar NLC tayi barazanar tsunduma yajin aiki a ƙasa baki ɗaya a cikin wata wasiƙa data aike wa shugaban ƙasa Buhari ranar Jumu'a, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Kwafin wasiƙar da aka aikewa hukumar dillancin labarai ta ƙasa NAN, ya nuna cewa shugaban NLC, Ayuba Waba, ya sanya hannu a kan wasiƙar.

NLC Ta Aike Wa Buhari Wasiƙa, Tayi Barazanar Sake Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa a Kan El-Rufa’i
NLC Ta Aike Wa Buhari Wasiƙa, Tayi Barazanar Sake Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa a Kan El-Rufa’i Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Wani ɓangaren wasiƙar yace: "Ranka ya daɗe, idan zaka iya tuna wa, mun yi taron sulhu na farko tsakanin NLC ta gwamnatin jihar Kaduna a ranar 20 ga watan Mayu 2021."

"NLC da gwamnatin Kaduna sun sanya hannu a kan wata yarjejeniyar fahimtar juna a taron, wadda ta ƙunshi cewa, gwamnatin ba zata sake taɓa ma'aikata ko yan kasuwa a jihar ba musamman waɗanda suka fito muka yi zanga-zanga tare."

KARANTA ANAN: Najeriya Zata Samar Da Manyan Wayoyin Hannu Ga Ƙasashen Africa, Pantami

"Amma abun mamaki, bayan amincewa da wannan, gwamnatin Kaduna tayi fatali da dukkan wannan yarjejeniya da aka cimma wa tsakaninta da ma'aikata."

Mr. Wabba ya cigaba da cewa matuƙar gwamnatin Kaduna ta cigaba da cin zarafin ma'aikata, kuma taƙi aiwatar da MoU da ta sanya wa hannu to zasu ɗauki mataki.

Yace majalisar ƙoli ta ƙungiyar NLC ta cimma matsaya cewa idan gwamnatin Kaduna ta tsaya kan bakarta na yaƙi da NLC, to zata sake sabunta yajin aikin data janye a jihar, sannan zata yi kira ga ma'aikatan Najeriya baki ɗaya su shiga yajin aiki.

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Yayi Murabus Daga Muƙamin Shugaban NBA

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari , ya sauka daga muƙamin shugaban NBA bayan ƙarewar wa'adinsa.

Buhari yayi godiya ga dukkan shugabannin ƙasashen da NBA ta haɗa bisa goyon bayan da suka nuna masa na tsawon shekara biyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel