Najeriya Zata Samar Da Manyan Wayoyin Hannu Ga Ƙasashen Africa, Pantami

Najeriya Zata Samar Da Manyan Wayoyin Hannu Ga Ƙasashen Africa, Pantami

- Ministan Sadarwa, Dr. Isa Pantami, yace Najeriya zata iya samar da manyan wayoyin hannu da layukan waya ga ƙasashen Africa

- Ministan yace nan da shekara 2 zuwa 3, kashi 60-70% na abubuwan da muƙe buƙata a ɓangaren sadarwa za'a samar dasu a cikin ƙasa

- Ministan ya bayyana haka ne a wajen wani taro da jam'iyyar APC ta shiryawa hadiman gwamnatin tarayya

Ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Dr. Isa Pantami yace Najeriya tana da damar da zata samar da layukan waya da manyan wayoyin hannu ga ƙasashen Africa, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaba Buhari Ya Gana da Gwamnan Cross Rivers, Ben Ayade, Bayan Komawarsa APC

Ministan ya faɗi haka ne a wani taro da jam'iyyar APC ta shirya ranar Alhamis a Sakateriyar jam'iyyar dake Abuja.

APC ta shirya taron ne ga hadiman gwamnati su baje kolin nasarorin da suka samu tun sanda suka shiga ofis ga yan Najeriya.

Yayin da Pantami ke jawabi a wajen taron, ya tabbatar da cewa daga yanzun za'a daina shigo da layukan waya daga ƙasashen waje da sauran kayan sadarwa saboda kashi 60-70% Najeriya zata rinƙa samar da su, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Najeriya Zata Samar Da Manyan Wayoyin Hannu Ga Ƙasashen Africa, Pantami
Najeriya Zata Samar Da Manyan Wayoyin Hannu Ga Ƙasashen Africa, Pantami Hoto: @FMoCDENigeria
Asali: Twitter

A cewar ministan Najeriya tana da ƙarfin da zata iya samar da layukan waya 200 miliyan duk shekara.

KARANTA ANAN: Babbar Magana: PDP Ta Buƙaci Wani Gwamna Yayi Murabus Daga Muƙaminsa

Pantami yace: "Munzo da sabon tsari wanda nan da shekara 2 zuwa 3, mafi karanci kashi 60-70% na abinda muke buƙata ta ɓangaren sadarwa zamu samar dashi a cikin gida Najeriya."

"Lokacin da wannan gwamnatin tazo, layukan waya bama iya yi sai an kawo mana daga waje. Amma yanzun gwamnatin tarayya ta baiwa masu zaman kansu damar su samar da layukan waya, ba wai ga ƙasa kaɗai ba harda kasashen Africa."

"Muna da ƙarfin da zamu iya samar da layukan waya 200 miliyan a shekara. Yanzu a Najeriya muna samar da manyan wayoyin hannu."

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Yayi Murabus Daga Muƙamin Shugaban NBA

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya sauka daga muƙamin shugaban NBA bayan ƙarewar wa'adinsa.

Buhari yayi godiya ga dukkan shugabannin ƙasashen da NBA ta haɗa bisa goyon bayan da suka nuna masa na tsawon shekara biyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262