Yanzu Yanzu: An tabbatar da Alkali Baba a matsayin sufeto janar na ‘yan sanda

Yanzu Yanzu: An tabbatar da Alkali Baba a matsayin sufeto janar na ‘yan sanda

- A ranar Juma'a, 4 ga watan Yuni, hukumar ‘yan sanda ta tabbatar da Alkali Baba, a matsayin babban sufeto janar na 'yan sanda (IGP)

- Da farko Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci wani taro da ya hada da wasu manyan mambobin majalisarsa da IGP din

- Maigari Dingyadi, Ministan harkokin 'yan sanda, ya fada wa manema labarai a karshen taron cewa majalisar ta tabbatar da IGP Baba

Hukumar 'yan sanda ta tabbatar da nadin Alkali Baba a matsayin babban Sufeto Janar na 'yan sanda (IGP), jaridar Leadership ta ruwaito.

Legit.ng ta tuna cewa a ranar 6 ga Afrilu ne Buhari ya nada Usman Baba a matsayin mukaddashin Sufeto Janar na 'yan sanda.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan PDP ya bayyana dalilin da yasa takwarorinsa ke komawa APC

Yanzu Yanzu: An tabbatar da Alkali Baba a matsayin sufeto janar na ‘yan sanda
Yanzu Yanzu: An tabbatar da Alkali Baba a matsayin sufeto janar na ‘yan sanda Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta kuma ruwaito cewa an yanke hukuncin ne a taron hukumar wanda shugaba Buhari ya jagoranta a ranar Juma’a, 4 ga watan Yuni, a Abuja.

Jaridar ta bayyana cewa Ministan harkokin 'yan sanda, Maigari Dingyadi, ya tabbatar da ci gaban ga manema labarai na Fadar Shugaban Kasa a karshen taron.

KU KARANTA KUMA: Dukanmu muna da laifi, in ji Obasanjo kan halin da Najeriya ke ciki

Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar ‘yan sanda

A yau Juma'a, 4 ga watan Yuni ne, Shugaban kasa Buhari ya jagoranci zaman majalisar ‘yan sanda a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Wadanda suka halarci taron sun hada da Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo; Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha.

Sauran wadanda ke halartar taron a zahiri su ne Shugaban Ma’aikatan Shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari; Ministan harkokin ‘yan sanda, Alhaji Maigari Dingyadi; Ciki, Ra’uf Aregbesola; Babban Birnin Tarayya (FCT) Muhammed Bello da Shugaban Hukumar Kula da ’Yan sanda (PSC), Musiliu Smith.

An kuma ga mukaddashin Sufeto-Janar na 'yan sanda, Usman Baba a wurin taron amma ba ya cikin tattaunawar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel