Fansar miliyan N110: Al’umman gari sun fara tattara kudi domin ceto daliban Islamiyya da aka sace a Neja
- Rahotanni sun kawo cewa al’umman garin Tegina, inda aka sace yara masu yawa sun fara tattara kudi domin ceto daliban Islamiyya da aka sace
- Shugaban makarantar Islamiyya, Salihu Tanko Abubakar Alhassan, ya ce wadanda suka sace yaran sun fara dukan yaran da ke hannunsu harma wasu basa iya tafiya
- Yan bindigar dai sun nemi a biya kudin fansa naira miliyan 110 kafin su saki yaran
Shugaban makarantar Islamiyya ta yara da ke Tegina inda aka sace dalibai da dama a kwanan nan ya ce wadanda suka sace yaran sun fara dukan yaran da ke hannunsu.
An tattaro cewa yawancinsu ba sa iya tafiya a yanzu.
Shugaban makarantar Islamiyyar, Salihu Tanko Abubakar Alhassan ya bayyana a cikin wata hira da aka yi da shi a gidan talbijin na Arise TV wanda jaridar The Nation ta bibiya cewa an sace uku daga cikin malamansa da suka hada da mata biyu da kuma namiji daya tare da yaran.
KU KARANTA KUMA: Hadimar Buhari ta wallafa hotuna yayinda yan sanda suka dakile yunkurin sace malamin addini a Kaduna
Daya daga cikin malaman mata "ta ce sun fara dukansu, ba abinci ko ruwa kuma cewa kafafun wasu daga cikin yaran sun kumbura kuma ba za su iya tafiya ba."
Alhassan ya ce daya daga cikin iyayen yaran da aka sace ta mutu a ranar Talata, inda ya kara da cewa danta daya tilo yana cikin wadanda aka sace.
Shugaban makarantar ya koka kan cewa gwamnatin jihar ba ta ziyarci iyayen ba.
“Halin da muke ciki yana da matukar damuwa. Ba mu karɓi wakilai don tausaya mana ba. Ko game da kudin fansar, ba mu samu amsa daga gare su ba.”
KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin kasa kadai ba za ta iya magance matsalar tsaron Najeriya ba – Shugaban hafsan soji
Al’umma sun fara tara kudade domin biyan fansar naira miliyan 110 da yan bindigar suka nema.
Jaridar The Nation ta samu labarin cewa san-kiran garin suna ta zagayawa cikin al'umma suna rokon mazauna garin da su ba da gudummawa domin ceto yaran da aka sace.
Mun Fara Tattaunawa da Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban Islamiyya, Gwamnatin Neja Tayi Ƙarin Haske
A baya Legit.ng ta kawo cewa gwamnatin jihar Neja ta bayyana cewa ta fara tattaunawar neman masalaha da yan bindigan da suka sace ɗaliban makarantar islamiyyar Salihu Tanko dake Tegina ƙaramar hukumar Rafi jihar Neja.
Gwamnatin tace ta fahinci an fara tattauna wa tsakanin yan bindigan da iyayen yaran, amma tace ita ba zata biya ko sisi da sunan kuɗin fansa ba.
Mataimakin gwamnan jihar, Muhammad Ketso, shine ya bayyana haka a Minna Ranar Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai, kamar yadda punch ta ruwaito.
Asali: Legit.ng