Dukanmu muna da laifi, in ji Obasanjo kan halin da Najeriya ke ciki

Dukanmu muna da laifi, in ji Obasanjo kan halin da Najeriya ke ciki

- Halin da ake ciki a Najeriya na neman wuce gona da iri, a cewar tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo

- A wata sanarwa da ya fitar a baya-bayan nan, Obasanjo ya ce an kadarci kasar da zama babbar kasa amma mummunan shugabanci ya zama babban cikas a gare ta

- A halin yanzu, tsohon shugaban kasar ya ce akwai bukatar sauya halin da Najeriya ke ciki

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya magantu a kan halin da kasar ke ciki kuma ya yanke shawarar cewa Najeriya ba ta a inda Allah ya kadarceta da kaiwa a cikin tsarin kasashe.

Ya koka kan cewa maimakon ta zama ƙasa mai yalwar madara da zuma, abin takaici ta zama "ƙasar da ke kwararar da ɗaci da baƙin ciki", yana mai roƙon ‘yan Najeriya da su sauya labarin, jaridar Punch ta rahoto.

KU KARANTA KUMA: Gumi ga FG: Ku sasanta da yan bindigar da suka tuba, ku yi amfani da su wajen yakar wadanda suka ki saduda

Dukanmu muna da laifi, in ji Obasanjo kan halin da Najeriya ke ciki
Dukanmu muna da laifi, in ji Obasanjo kan halin da Najeriya ke ciki Hoto: The Nation
Asali: UGC

Tsohon Shugaban kasar ya yi magana ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a Cibiyar Matasa ta dakin karatun shugaba Olusegun Obasanjo (OOPL), Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun, yayin gabatar da wani littafi Mai taken: ‘The Man General President Olusegun Obasanjo, GCFR’.

An rubuta shi ne don girmama Obasanjo da kuma bikin murnar cikarsa shekaru 84 da haihuwa, jaridar The Nation ta ruwaito.

Obasanjo ya lura cewa Allah ne ya halicci Najeriya don jagorantar bakaken fata, yana mai takaicin cewa kasar ba ta dace da wannan matsayin ba saboda gazawar shugabanci.

“Aikin da ke gabanmu yanzu shi ne tunanin gudummawar da za mu bayar don mai da Najeriya abin da Allah ya halicceta ta zama, kasar da ke malala da madara da zuma. A yanzu haka, ƙasa ce mai gudana da ɗaci da baƙin ciki. Ba haka Allah Ya nufa ga ƙasar nan ba. Dole ne mu canza shi. Kuma dole ne mu canza labarin.”
Game da abin da ya kamata a yi don kawar da mummunan halin, Obasanjo ya ce: "Ina matukar farin ciki cewa muna da mutane da yawa a cikin kasarmu kuma a zahiri a wajen kasarmu da suka yi imani da kimar ilimi…
"Idan ba shakka za mu kai kasar nan ga inda Allah ya halicce ta kasance, domin inda muke yanzu ba inda Allah ya halicci Najeriya ta kasance bane, to dole ne ilimi ya zama daya daga cikin manyan ginshikan kai Najeriya ga inda ya kamata.
“Kuma sama da yara miliyan 14 da yanzu ba sa zuwa makaranta, dole ne mu nemi hanyar komawa makaranta. In ba haka ba, muna shirya Boko Haram na gobe kuma babu abin da zai hana hakan. Idan ba mu yi yanzu ba, za mu rasa dama kuma sakamakonsa yana nan gaba. Ta yiwu wasu daga cikinmu sun shude amma wasu daga cikin waɗanda za su kasance a raye za su ɗauki nauyin matsala.
“Babu wani abin da za mu iya yi game da hakan. Na yi imanin cewa Allah ne ya halicci Najeriya don jagorantar baƙar fata.
“Cewa ba ma aikatawa ba wai don saboda Allah bai bamu dukkan abin da muke bukata don aikatawa bane. Saboda mun gaza ne ta bangaren shugabanci. Kuma dole ne a gyara hakan. Gaskiyar ita ce, laifin dukkanmu ne. Ya kamata mu yi magana, ya kamata mu yi magana. Kuma ya kamata ka fadi abin da ya kamata ka fada kuma ka fadi a lokacin da ya kamata ka fade shi.”

A wani labarin, shugaban cocin Citadel Global Community wanda a baya aka sani da Latter Rain Assembly, Tunde Bakare, ya ce sam shugaban kasa ba ya sauraronsa.

Jaridar The Cable ta ce Fasto Tunde Bakare ya koka a kan cewa shugaba Muhammadu Buhari ba ya daukar maganganun da ya fada masa domin kawo gyara.

Tunde Bakare wanda ya yi takarar kujerar mataimakin shugaban kasa tare da Muhammadu Buhari a CPC ya ce ya gaji da zama da shugaban Najeriyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel