Musulmi Na Da Kotun Musulunci, Muma a Bamu Kotun Kirista, Ƙungiyar CAN Ta Jihar Bauchi

Musulmi Na Da Kotun Musulunci, Muma a Bamu Kotun Kirista, Ƙungiyar CAN Ta Jihar Bauchi

- Kungiyar kirista ta Nigeria wato CAN reshen jihar Bauchi ta nemi a kafa kotunan kirista

- CAN ta ce idan har ana son yin adalci ya kamata a basu kotuna da hukuma kamar yadda aka yi wa musulmi a jihar

- Kungiyar ta kiristocin ta ce yin hakan shine zai zama adalci a wurinsu domin addinin kirista na daga cikin manyan addinai a kasar

Kungiyar kirista ta Nigeria, CAN, reshen jihar Bauchi ta bukaci a kirkiri kotun na musamman domin kiristoci kamar yadda akwai kotunan shari'ah domin musulmi, tana mai mai cewa hakan zai tabbatar da warware matsaloli tsakanin malaman addini da sauran kiristoci, rahoton Vanguard.

A wani rubutu da ta gabatar wa kwamitin majalisar wakilai na tarayya da aka kafa domin yi wa kundin tsarin mulkin 1999 garambawul, a ranar Alhamis, CAN ta janyo hankalin mutane kan sashi na 10 na kudin tsarin mulki da ya ce gwamnatin tarayya ko jiha ba za ta iya amfani da kowane addini a matsayin doka ba amma anyi watsi da wannan sashi.

Musulmi Na Da Kotun Musulunci, Muma a Bamu Kotun Kirista, Ƙungiyar CAN Ta JIhar Bauchi
Musulmi Na Da Kotun Musulunci, Muma a Bamu Kotun Kirista, Ƙungiyar CAN Ta JIhar Bauchi. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: 'Yan Bindiga Sun Fara Yin Kaka-gida a Dazukan Kano, Ganduje

CAN, ta bakin wakilinta, Barista Bichi Obadiah ta ce, "Amfani da wani addini guda a dokokinsa a bisa sauran addinai ya saba wa abinda kundin tsarin mulki ya tanada.

"Misali, a jihar Bauchi, an yi tanadin kafa kotunan Shari'ah tun 2000/2001. Hasali ma, an kirkiri hukuma ta shari'a an kuma kafa kotunan shari'a da suka maye gurbin kotuna da ake da su a yankunan.

"Kafa kotunan shari'a da hukuma ta shari'a ta tare da kafa na kirista ba wariyya ne kuma hakan na iya janyo rikici wurin samun aiki domin dukkan ma'aikatan kotunan shari'a da hukumar musulmai ne."

KU KARANTA: Ana Iya Tura Masu Yi Wa Ƙasa Hidima Filin Daga Suyi Yaƙi, Shugaban NYSC

CAN ta kuma bada shawarar a yi garambawul ga dokar ya zama cewa an soke duk wani doka na tarayya ko jiha da ya bada daman kafa kotu ko hukumar shariah ba tare da kafa na kirista ba.

A cewar kungiyar ta CAN, kirista na daga cikin manyan addinai a kasar don haka ya kamata duk wani doka da za a yi a rika la'akari da su tare da bukatunsu.

A wani labarin daban, Hukumar Yaki Da Hana Safarar Miyagun Kwayoyi na Kasa, NDLEA, ta ce ta kama wasu mutane da ake zargi da safararmiyagun kwayoyi a birnin tarayya Abuja, The Cable ta ruwaito.

Femi Babafemi, kakakin NDLEA, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ya ce an kama su ne sakamakon samamen da hukumar ta yi cikin wannan makon.

Cikin wanda aka kama akwai wata Ese Patrick da ake zargi na siyar da miyagun kwayoyi a dandalin Instagram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel