'Yan Bindiga Sun Fara Yin Kaka-gida a Dazukan Kano, Ganduje

'Yan Bindiga Sun Fara Yin Kaka-gida a Dazukan Kano, Ganduje

- Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan Kano ya koka kan yadda yan bindiga ke mamaye dazukan jiharsa

- Ganduje ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kaiwa sabon shugaban sojoji Manjo Janar Farouk Yahaya

- Gwamna Ganduje ya roki rundunar ta sojoji ta yi gaggawan cigaba da aikin da ta fara a dajin Falgore na gina sansanin bada horaswa

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa yan bindiga sun fara mamaye dazukan jiharsa kuma akwai yiwuwar suna shirin kai hare-hare ne, Tha Nation ta ruwaito.

The Punch ta ruwaito cewa gwamnan ya yi wannan furucin ne a Hedkwatar Tsaro inda ya gana da shugabannin sojoji, ya ce yan bindigan na taruwa a dajin Falgore duk da jihar na kokarin bude dazukan.

'Yan Bindiga Sun Fara Taruwa a Dazukan Jihar Kano, Ganduje
'Yan Bindiga Sun Fara Taruwa a Dazukan Jihar Kano, Ganduje. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Da Ɗuminsa: Soja Ya Bindige Jami'an Kwastam Har Lahira a Seme Border

Duk da cewa ya bada tabbacin gwamnatinsa da hukumomin tsaro za su cigaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya a jihar, gwamnan yayin ganawa da babban hafsan sojojin kasa, Manjo Janar Farouk Yahaya, ya roki sojojin su yi gaggawar aikin kafa sansanin horas da sojoji a dajin Falgore don sojoji su karbe dajin.

Ganduje ya ce zaman lafiyar da ake samu a jiharsa ta samu ne bisa kyakyawar alaka da ke tsakanin gwamnatinsa da hukumomin tsaro.

A cewarsa, "Na kawo ziyara ne don jajantawa sojoji bisa rasuwar tsohon shugaban hafsin sojojin kasa Laftanat Janar Ibrahim Attahiru da wasu jami'ai 10. Abu ne mai ciwo amma munyi tawakkali duba da cewa sun rasu ne yayin yi wa kasarsu hidima. Na kuma zo nan ne don neman taimakon Rundunar Sojojin Nigeria wurin tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano; yan bindiga sun mayar da wasu dazukan jihar mabuyarsu.

"Muna gina gidaje, makarantu da asibitoci domin makiyaya a wasu dazukan amma duk da haka muna son sojoji su fara aiki a dajin Falgore."

KU KARANTA: Hotunan Muggan Makaman Da Ƴan Sanda Suka Ƙwato Daga Hannun Masu Garkuwa Da Ƴan Bindiga

A jawabinsa, babban hafsan sojojin na kasa, ya yi alkawarin zai ziyarci Falgore domin ganin yadda za a cigaba da ayyukan sojoji a dajin.

Ya ce rundunar sojoji da sauran hukumomin tsaro za su cigaba da ganin sun dakile kallubalen tsaro a kasar.

A wani labarin daban, daliban makarantun sakandare a jihar Kano sun yi kira ga gwamnatin jihar ta samarwa dalibai mata audugan mata kamar yadda ta ke samar da littafan karatu kyauta, Vanguard ta ruwaito.

Daliban sun koka da cewa yan mata da yawa ba su da kudin siyan audugan matan, don haka suke rokon gwamnatin ta taimaka musu domin su samu su rika tsaftace kansu.

Sun yi wannan rokon ne yayin wani taron wayar da kai na kwana daya da aka yi kan tsaftar mata da jiki da Kungiyar Yan Jarida Masu Rahoto Kan Bangaren Lafiyar Mata reshen jihar Kano suka shirya don bikin ranar Al'adar Mata Ta Duniya na 2021'

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel