Rundunar sojin kasa kadai ba za ta iya magance matsalar tsaron Najeriya ba – Shugaban hafsan soji

Rundunar sojin kasa kadai ba za ta iya magance matsalar tsaron Najeriya ba – Shugaban hafsan soji

- Sabon shugaban rundunar soji na kasa, Manjo Janar Farouk Yahaya, ya jadadda cewa sojin kasa kadai ba za su iya magance matsalar tsaron Najeriya ba

- COAS din ya ce akwai bukatar hada kai tsakanin dukkanin rundunonin soji da sauran hukumomin tsaro domin nasara wajen yaki da ta'addanci

- Ya kuma ce rawar ganin da rundunar sojin sama ke takawa a yaki yana da matukar muhimmanci duba ga tasirin da hakan yayi a yaki daban-daban

Babban hafsan soji, Manjo Janar Farouk Yahaya, a ranar Laraba, ya ce sojojin kasa kadai a cikin rundunar soji ba za su iya shawo kan babban kalubalen tsaro da ke addabar kasar ba.

Shugaban sojin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga takwaransa na sojin sama, Air Marshal Oladayo Amao, a Hedikwatar Sojin Saman Najeriya, Abuja.

KU KARANTA KUMA: Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Yan Fulani a Jihar Kwara

Rundunar sojin kasa kadai ba za ta iya magance matsalar tsaron Najeriya ba – Shugaban hafsan soji
Rundunar sojin kasa kadai ba za ta iya magance matsalar tsaron Najeriya ba – Shugaban hafsan soji Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

A cewarsa, runduna daya ba za ta iya cin nasarar yaki da masu tayar da kayar baya da 'yan fashi da makami ba sai dai ta hanyar hadin kai, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya kara da cewa rundunar sama na da matukar muhimmanci a yakin da ke gudana kan ta’addanci, fashi da makami da sauran laifuka a kasar.

"Tun da farko duk mun fahimci cewa babu wata runduna da za ta iya yin hakan ita kadai, zai fi kyau a gare mu aiki tare a matsayin rundunonin soji da Kasa don shawo kan kalubalen tsaro da ake ciki a yanzu," in ji COAS.

Shugaban sojin ya jaddada cewa shi ya kasance mai ba da shawara game da samar da rundunar sama a matsayin muhimmiyar bukata ta rundunar yaki duba da gagarumin tasirin da take da shi a yaki daban daban, Naijanews ta ruwaito.

A nasa bangaren, CAS, Amao ya taya COAS murna kan nadin da aka yi masa sannan ya bukace shi da ya ci gaba da hada karfi da karfe a kokarin da Sojojin Najeriya da NAF ke yi, tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro don kawar da kasar daga dukkan ayyukan ta'addanci.

KU KARANTA KUMA: Bishop Kuka yayi kira ga shugabannin Najeriya da su daina daukar rantsuwar da basu kiyayewa

A wani labarin, mun ji cewa Shugaban sojin kasa na Najeriya, Manjo Janar Farouk Yahaya ya jinjinawa kokarin dakarun sojin kasan Najeriya dake aiki wurin Sabon Birni, garin da ke iyakar jihar Sokoto.

Dakarun sojin sun yi musayar wuta da wasu da ake zargin dillalan bindigogi ne kuma sun kashe mutum ukun tare da samo miyagun makamai daga wurinsu.

Wannan jinjinar na dauke ne a wata takarda da daraktan hulda da jama'a na rundunar, Birgediya Janar Mohammed Yerima ya wallafa a Twitter sannan ya mika ga manema labarai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel