Kawai mu rufe majalisar dokokin tarayya idan har ba za mu iya ceto kasar ba – Sanata Smart Adeyemi

Kawai mu rufe majalisar dokokin tarayya idan har ba za mu iya ceto kasar ba – Sanata Smart Adeyemi

- Halin da Najeriya ke ciki ya batawa Sanata Smart Adeyemi rai har ya kusan yin kuka yayin da yake magana da abokan aikin sa

- A cewar dan majalisar daga jihar Kogi, dole ne majalisar kasa tayi wani abu game da lamarin ko kuma su rufe majalisar

- Da yake ci gaba, ya ce babu bukatar ‘yan majalisar su yi kamar basu san halin da ake ciki ba, inda ya dage cewa kasar na zubar jini

Sanatan da ke wakiltar Kogi ta Yamma a Majalisar Tarayya, Sanata Smart Adeyemi ya yi kira ga takwarorinsa da su rufe majalisar idan ba za su iya magance matsalolin kasar ba.

KU KARANTA KUMA: Fansar miliyan N110: Al’umman gari sun fara tattara kudi domin ceto daliban Islamiyya da aka sace a Neja

Kawai mu rufe majalisar dokokin tarayya idan har ba za mu iya ceto kasar ba – Sanata Smart Adeyemi
Kawai mu rufe majalisar dokokin tarayya idan har ba za mu iya ceto kasar ba – Sanata Smart Adeyemi Hoto: Punch
Asali: UGC

Sanatan ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a zauren majalisa a cikin wani bidiyo da jaridar Legit.ng ta gani kuma jaridar Punch ta buga.

Ya ce:

"Kawai mu rufe majalisar kasa idan har ba za mu iya samar da tsaro ga kasar nan ba. Kasar mu tana zubda jini. Mutane suna cikin talauci. Mutane suna jin yunwa. Ba za mu iya yi kamar bamu san halin da ake ciki ba, kowace rana, mutane suna mutuwa. Dole ne mu tashi tsaye."

A wani labarin, Lai Mohammed, ministan yada labarai, ya ce ayyukan da Ahmed Gumi, mashahurin malamin addinin Islama ya ke yi, ba za a iya kwatanta su da na Nnamdi Kanu ba, shugaban kungiyar da ke ikirarin ballewa daga kasa.

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin kasa kadai ba za ta iya magance matsalar tsaron Najeriya ba – Shugaban hafsan soji

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin zantawarsa da manema labarai na fadar gwamnati a Abuja.

Mohammed yana amsa tambaya ne a kan dalilin da ya sa Gumi - wanda ya yi kira a yi afuwa ga ‘yan bindiga - gwamnatin tarayya ba ta bayyana cewa tana neman sa ruwa a jallo ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel