Babbar Magana: PDP Ta Buƙaci Wani Gwamna Yayi Murabus Daga Muƙaminsa
- Jam'iyyar hamayya ta PDP reshen jihar Imo tayi kira ga gwamnan jihar yayi murabus daga kujerarsa
- PDP tace gwamnan bashi da karsashi ko ƙwarin guiwar da zai fuskanci matsalar tsaron da take kara yawaita a jihar
- Jam'iyyar ta kuma sake yin kira da a gudanar da bincike mai zurfi a kan kisan da akai wa Ahmed Gulak, tsohon hadimin shugaba Jonathan.
Babbar jam'iyyar hamayya PDP, reshen jihar Imo ta kira yi gwamnan jihar, Hope Uzodinma, yayi murabus daga kan kujerarsa saboda ƙaruwar matsalar tsaro a jihar, kamar yadda Punch ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaba Buhari Yayi Murabus Daga Muƙamin Shugaban NBA
A wani taron manema labarai a Owerri, babban birnin jihar, shugaban PDP na jihar Imo, Charles Ugwu, yace ga dukkan alamu gwamnan bashi da ta cewa a kan kashe-kashen dake faruwa a jihar.
PDP tayi kira da a gudanar da bincike mai zurfi kan kisan tsohon hadimin shugaban ƙasa, Ahmed Gulak, da akayi a jihar ranar Lahadi da safe.
Agwu yace gwamnatin jam'iyyar APC bata da karsashin da zata tabbatar da tsaron lafiyar al'umma da kare dukiyoyinsu.
KARANTA ANAN: Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban Islamiyya a Neja Zasu Ƙara Ƙudin Fansa
Yace: "Gwamna Hope Uzodinma, a matsayinsa da abunda ya rataya a wuyansa amma ya gaza kare al'umma da dukiyoyinsu a jihar Imo."
"Wannan abu ne a bayyane, gwamnatin APC ta gaza tabbatar da kare rayukan mutanen ta da dukiyoyin su duba da irin abubuwan dake faruwa a jihar."
Shugaban PDP ɗin yace an jawo hankalin jam'iyyar su cewa ana kama wa tare da kashe matasan jihar da basu ji ba basu gani ba.
Ugwu ya ƙara da cewa PDP ta damu matuƙa da irin cin mutuncin da akewa matasan jihar da kuma ƙona ofishin INEC da Caji Ofis.
A wani labarin kuma Mahaifiyar Ɗaya Daga Cikin Ɗaliban da Aka Sace a Islamiyya Ta Rigamu Gidan Gaskiya
Ɗaya daga cikin iyayen ɗaliban islamiyyar jihar Neja da aka sace ɗalibanta ta rigamu gidan gaskiya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Mahaifiyar ta yanke jiki ta faɗi lokacin da aka shaida mata labarin abinda ya faru na satar Yaran.
Asali: Legit.ng