Hadimar Buhari ta wallafa hotuna yayinda yan sanda suka dakile yunkurin sace malamin addini a Kaduna

Hadimar Buhari ta wallafa hotuna yayinda yan sanda suka dakile yunkurin sace malamin addini a Kaduna

- Rundunar ‘yan sandan Nijeriya a ranar Laraba, 2 ga watan Yuni, ta kame tare da gurfanar da wasu da ake zargin suna da alaka da yunkurin yin garkuwa da wani malamin addinin kirista

- Lauretta Onochie, daya daga cikin hadiman shugaba Buhari kan harkokin yada labarai, ta bayyana cewa an yi kamun ne a Kaduna

- Onochie ta kuma bayyana cewa yan sanda sun damke akalla masu laifi 84 sannan kuma suka kwato makamai daga hannun su

Jami’an ‘yan sanda sun dakile wani yunkuri da wasu masu satar mutane dauke da makami suka yi na sace wani limamin cocin Katolika a Zariya, jihar Kaduna a ranar Laraba, 2 ga watan Yuni.

Da take bayar da wannan bayanin, mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Lauretta Onochie, ta shafin ta na Twitter, ta ce nasarar da rundunar ta samu ya kasance ne sakamakon sabon tsarin aikin tsaro da ke aiki a yanzu don tabbatar da tsaron 'yan Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin kasa kadai ba za ta iya magance matsalar tsaron Najeriya ba – Shugaban hafsan soji

Hadimar Buhari ta wallafa hotuna yayinda yan sanda suka dakile yunkurin sace malamin addini a Kaduna
Hadimar Buhari ta wallafa hotuna yayinda yan sanda suka dakile yunkurin sace malamin addini a Kaduna Hoto: @Laurestar
Asali: Twitter

Onochie ta ce zuwa yanzu ‘yan sanda sun yi amfani da wannan gagarumin dabara wajen cafke akalla masu laifi 84 a fadin kasar a cikin wata daya.

Ta bayyana cewa daga cikin bindigogin da jami’an tsaro suka kwato a yayin gudanar da ayyukansu akwai GPMG guda daya, karamar bindiga kirar LAR, bindigogin AK47 17, bindigogin Pump Action guda biyu, bindigogin gida 20, bindigogi guda uku, albarusai masu rai 9899, lambar motocin bogi 80 da kuma Toyota Camry AA 792 HJA1 daya da Toyota Corolla LE mai lamba QAP 622 AA.

KU KARANTA KUMA: Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Motar Bas Ta Makaranta a Ondo

Yan bindiga sun kashe limamin Katolika, sun sace wani a Katsina

A wani labarin, wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe wani limamin katolika, Rev. Fr. Alphonsus Bello, yayinda suka yi garkuwa da wani, Rev. Fr. Joe Keke a cocin St. Vincent Ferrer Catholic Church Malunfashi, jihar Katsina.

An tattaro cewa yan bindigan, a daren ranar Alhamis, sun afkawa cocin Katolika sannan suka fara harbi ba kakkautawa a iska, lamarin da ya jikkata wasu mutane.

Daraktan sadarwa na Sakatariyar Katolika ta Najeriya, Padre Mike Umoh, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce wadanda ake zargin sun jefar da gawar Fr Alphonsus Bello a cikin gonar da ke bayan Makarantar Horarwa ta Catechetical, Malunfashi yayin da har yanzu ba a san inda Fr. Joe Keke yake ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel