Karin Bayani: Yan Bindiga Sun Sako Ma'aikaciyar Makaranta da Suka Kama Ondo

Karin Bayani: Yan Bindiga Sun Sako Ma'aikaciyar Makaranta da Suka Kama Ondo

- Yan bindiga sun sako ma'akaciyar dake cikin motar bas ɗin da suka yi awon gaba da ita a Ondo

- Ma'aikaciyar mai suna, Omolayo Ojo, tace sun tambayeta sunanta, daga baya kuma suka umarce ta da ta ruga kada ta waigo

- A halin yanzun, shugabar makarantar tace lamarin na hannun yan sanda, zasu cigaba da bincike a kan shi

Omolayo Ojo, ma'aikaciya a makarantar Chimola School, Akure, jihar Ondo, wacce yan bindiga suka yi awon gaba da ita da Motar Bas ranar Alhamis da safe, ta kuɓuta.

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Mahaifiyar Ɗaya Daga Cikin Ɗaliban da Aka Sace a Islamiyya Ta Rigamu Gidan Gaskiya

Legit.ng hausa ta gano cewa maharan sun rasa damar su saboda babu ɗaliban makarantar a cikin motar.

Da take magana bayan ƙuɓutar ta, Ojo ta bayyana cewa yan bindigan sun yi barazanar cutar da ita idan bata basu haɗin kai ba, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Saki Motar Bas Ta Makaranta da Suka Kama a Ondo
Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Saki Motar Bas Ta Makaranta da Suka Kama a Ondo Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Tace ta bi dukkan wani umarnin su, daga baya sai suka sake ta bayan sun gano ba ta da laifin komai, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Ojo tace sun tafi da ita zuwa wani wuri da bata san shi ba, amma ta samu hanyar dawowa Akure bayan ta tambayi mutanen da ta haɗu da su akan hanya.

KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Yan Fulani a Jihar Kwara

A cewar Ojo: "Naga ɗaya daga cikinsu ya fito da bindiga wani kuma ya zaro wuƙa. Da suka tare mu sun fitar da direban, suka rufe mun idona sannan suka jani zuwa cikin daji ba tare da nasan inda ake tafiya ba."

"Yayin da muka isa cikin dajin, sai suka buɗemun idanu na, suka tambayeni sunana, kuma suka ce inyi duk abinda suka Umarce ni."

"Daga baya sai suka ce in ruga da gudu kada in sake in waigo baya, akan hanya naga wata tsohuwa na tambayeta, ta nuna mun hanyar da zata kaini kan titi. Wani ɗan Okada ne ya bani N500 kuma ya nuna mun hanyar zuwa wani gari inda zan hau mota zuwa Akure."

Shugaban makarantar Mrs. Akinde Bolatito, tace direban ya faɗi mata duk abinda ya faru a caji ofis, inda yake cigaba da amsa tambayoyi.

Tace: "Omolayo ta daɗe tana aiki damu sama da shekara biyu nan baya. Sun tafi da ita zuwa cikin daji amma basu cutar da ita ba."

"Babu kowa a cikin motar bas ɗin, bamu taɓa samun matsala makamancin wannan ba. A halin yanzun yan sanda na bincike."

A wani labarin kuma Sama da Yan Najeriya 10,000 Sun Kamu da Rashin Lafiya Bayan an Musu Rigakafin COVID19 Kashi Na Farko

Hukumar Lafiya a matakin farko NPHCDA ta bayyana cewa yan Najeriya sama da 10,000 ne suka sami matsala bayan yin rigakafin korona.

Shugaban NPHCDA, Dr Faisal Shu'aib shine ya bayyana haka a babban birnin tarayya Abuja ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel