Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Motar Bas Ta Makaranta a Ondo

Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Motar Bas Ta Makaranta a Ondo

- Wasu 'yan bindiga sun afkawa motar makaranta, in da suka yi awon gaba da ma'aikaciyar makarantar

- Rahotanni sun bayyana cewa, motar na kan hanyarta na dauko daliban makarantar ne da sanyin safiya

- Rundunar 'yan sandan jihar Ondo bata tabbatar da faruwar lamarin ba, amma ta bayyana cewa ana kan bincike

Wasu ‘yan bindiga sun sace wata motar makaranta a Oba Ile Estate, karamar hukumar Akure ta Arewa a jihar Ondo, Daily Trust ta ruwaito.

Ko da yake babu wani dalibi da ke cikin motar, amma an ce maharan sun tafi da wata jami'ar makarantar da ke kan hanyarta ta zuwa daukar daliban daga gidajensu a safiyar Alhamis.

KU KARANTA: Ku kula, 'yan ta'addan IPOB sun shiga jihar Edo, suna shirya barna, in ji DIG

Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Motar Bas Ta Makaranta
Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Motar Bas Ta Makaranta Hoto: merar.com
Asali: UGC

A cewar wani mazaunin garin, ‘yan bindigan wadanda ke kan babura, sun tare motar ne da misalin karfe 6:45 na safe.

Wata majiya a cikin makarantar ta ce ‘yan bindigan wadanda yawansu ya kai takwas, sun yi kan wadanda abin ya shafa ne a kan babura, inda suka tilasta motar bas din da direbanta suka tsaya.

Ya ce masu garkuwan wadanda suke dauke da bindigogi, adduna da wasu makamai, sun sauko da direban daga motar suna barazanar kashe shi, in ji jaridar Guardian.

A cewarsa, bas din mai lambar: Lagos LSD 853 FJ, dauke da rubutun “Chimola Schools”, dayan maharan ne ya tuka ta yayin da wasu suka gudu a kan babura.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar (PPRO), Mista Tee-Leo Ikoro, yayin da aka tuntube shi, ya ce ba a yi masa bayani ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto, amma ya yi alkawarin tabbatarwa daga jami'in' yan sanda na shiyya da ke yankin.

KU KARANTA: Ba Dan Najeriya Mai Hankali Da Zai So Mulkin Dan Kudu Maso Gabas, Sumaila

A wani labarin, Wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun kai hari bankunan kasuwanci biyu da ofisoshin ‘yan sanda da yammacin Laraba a garin Apomu da Ikire da ke jihar Osun.

A yayin harin, an samu labarin cewa ‘yan fashin sun harbe mutane da yawa, duk da cewa rundunar 'yan sanda ta jihar ta ce ba ta samu adadin wadanda suka rasa rayukansu ba.

An ce barayin sun shiga Apomu da Ikire ta cikin garin Ikoyi kuma sun kasa kansu zuwa gungu daban-daban kafin su fara kai hari kan ofisoshin ‘yan sanda da bankunan da abin ya shafa, jaridar Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel