Garba Shehu Ya Yabawa Gwamna Ganduje, Ya Gamsu Da Ci Gaban Da Kano Ta Samu
- Mataimakin shugaban kasa kan yada labarai ya yaba da ci gaban da gwamnatin Ganduje ta kawo
- Ya ce duk masu kushe da suka ga gwamnatin a baya, yanzu sun cika da zunzurutun nadama
- Ya kuma shawarci 'yan jarida da su tsarkake ayyukansu da yada labarai da zasu dinke baraka
Garba Shehu, babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce wadanda suka yiwa gwamnan jihar Kano tawaye a baya yanzu haka suna cike da nadama, Daily Nigerian ta ruwaito.
Da yake jawabi a lokacin bude taron shekara ta 2021 na kungiyar Editocin Najeriya ranar Litinin a Kano, Shehu ya ce jihar ta samu ci gaba da yawa, cika alkawura da kuma sulhu a karkashin jagorancin Ganduje.
Ya bayyana cewa 'yan Najeriya na bukatar a basu kwarin gwiwa cewa gwamnatoci a dukkan matakai na aiki kai tsaye don kawo karshen rashin tsaro don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama'a.
KU KARANTA: Abubuwa 4 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Tsohon Hadimin Jonathan, Marigayi Ahmad Gulak
Ganin yadda labaran karya da tada hankali suka yi yawa a Najeriya, Mista Shehu ya yi kira ga editoci a wurin babban taron da su ci gaba da inganta zaman lafiya da hadin kai ta hanyar rahoton da suke bayarwa ta kafafen yada labarai, PM News ta kawo.
Ya kuma kalubalanci editocin da su yi amfani da muhimmiyar rawar da suke takawa wajen dinke barakar da ke tsakanin gwamnati da jama'a, musamman ta fuskar yada labarai.
“Ina ganin lokaci ya yi da za mu sa ido mu ga yadda za mu dakatar da yada labaran karya, sakaci da jita-jita.
“Ina ganin ya kamata mu ma mu yi amfani da wannan damar don tunatar da kawunanmu nauyin da ke kanmu na inganta aikin jarida," in ji Shehu.
KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: Dole Masu Rubuta Jarrabawar JAMB Su Biya N700 Kudin 'Mock'
A wani labarin, Fadar shugaban kasa ta bayyana kudirin ta na daukar nauyin shirin samar da gidaje na kasa (NSHP) don tallafawa 'yan Najeriya sama da miliyan 1.5.
A cikin wata sanarwa da Legit.ng ta samo, fadar shugaban ta ce gwamnatin tarayya tare da goyon bayan ma’aikatar kudi ta kammala shirye-shirye tare da Babban Bankin Najeriya don daukar nauyin wannan katafaren aikin.
Da yake magana kan aikin, Laolu Akande, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai ya ce manufar ita ce ‘yan kasa su mallaki gidaje masu rahusa ta hanyar jingina da kuma bayar da haya ga zabin mallaka.
Asali: Legit.ng