Dan Ba Kara: Dillalan Albasa 'Yan Arewa Sun Haramta Kai Wa 'Yan Kudu Albasa
- Kungiyar manoma da kasuwancin Albasa sun bayyana kauracewa kaiwa jama'ar kudu maso gabas kaya
- Kungiyar ta koka kan irin asarar 'yan IPOB ke jawo wa mambobinta, tare da yawaitar rashin tsaro
- Rashin tsaro na kara ta'azzara a yankin kudu maso gabas, in da ake zargin 'yan IPOB da aikata ta'addanci
Kungiyar masu noma Albasa da Kasuwancinta a Najeriya (OPMAN) ta bayyana kudurin ta na dakatar da samar da albasa ga yankin Kudu maso Gabas saboda yawaitar rashin tsaro.
Shugaban kungiyar OPMAN na kasa, Aliyu Isah, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba 2 ga watan Yuni, Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce kungiyar ta yanke shawarar ne biyo bayan sace motocin mambobinsu biyu da ‘yan bindiga suka yi wadanda suke zargin mambobin kungiyar masu fafutukar kafa haramtacciyar kasar Biafra ce ta IPOB suka aikata.
KU KARANTA: Ba Sauran Cece-Kuce: Majalisa Ta Amince Da Daidaita Kwalin HND Da Na Digiri
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin‘ yan kungiyar IPOB ne suna ta kai hare-hare kan muhimman kayayyakin more rayuwar jama’a a yankin kudu maso gabas na wasu makwanni tare da kashe jami’an tsaro da lalata kadarorin gwamnati.
A makon da ya gabata, sun yi awon gaba da manyan motoci biyu cike da albasa da suka taso daga Arewa a cikin jihar Imo tare da rarraba abubuwan da ke ciki ga jama’arsu.
A wata hira da sakataren kungiyar, Halilu Muhammad, ya bayyana karara yadda 'yan ta'addan suka tsare motocin tare da jawo musu mummunar asara.
KU KARANTA: Baya Ga Korona, Wata Sabuwar Cuta Ta Sake Bullowa a Kasar China Daga Kajin Gona
'Yan bindigan sun kuma kona gidan Kenneth tare da lalata motocin dan uwansa, wanda aka ce soja ne mai ritaya.
Lamarin da ya faru a Umuokwe, Eziawo 1, a cikin karamar hukumar, ya kara tayar da hankali a yankin.
Asali: Legit.ng